Kasancewar matasa ƙashin bayan al’umma wanda kuma suka fi fuskantar haɗarin amfani da su wajen cimma muradun miyagun ‘yan siyasa, Gamayyar Matasan Arewa a Kudu da ke Legas, ta yi kira da babbar murya ga ɗaukacin matasan Nijeriya da kar su bari ɓata-garin ‘yan siyasa su riƙa amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa musamman a halin yanzu da aka shiga kakar siyasa.
Gamayyar ta yi kiran ne ta hannun shugabanta, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci a wani ɓangare na yunƙurin da take yi wajen wayar wa da ‘yan ƙasa kai a game da abubuwan da za su kawo musu ci gaba a rayuwarsu.
A cewar gamayyar, “muna sake tunatarwa ga dukkan matasan Nijeriya da su guji yin bangar siyasa domin rayuwarsu tana cikin haɗari, ɓata-garin ‘yan siyasar ƙasarmu ba za su tsinana musu komai ba illa su yi ɗibga musu kayan maye saboda gusar da hankulansu, domin sun san cewa idan matasan suna cikin hayyacinsu ba za su iya saka su miyagun abubuwa ba a ƙoƙarinsu na cimma burinsu na son zuciya.”
Ƙungiyar ta ce irin yadda ake amfani da ƙazaman kuɗaɗe wajen tsayar da ‘yan takara a jam’iyyu manuniya ce kan irin lalacewar da tsarin siyasar ƙasar nan ya yi.
“Kun ga dai yadda ake sayen daliget, wannan shi ne ya nuna wa duniya cewa tsarin zaɓenmu ya gurɓace. ‘Yan siyasar sun mayar da sha’anin takara na ko-a-mutu-ko-a-yi-rai, sannan duk abubuwan da suke faruwa a arewa na kisan jama’a da sace-sacen dukiyoyinsu da cin zarafin iyalai akwai alamun wasu da ke kan mulki a madafun ikon gwamnati suna da hannu a ciki, haka nan wasu masu neman tsayawa takara, shi ya sa wasu ko ana-ha-maza-ha-mata za su ce dole su ci zaɓe domin rufe asirin miyagun ayyukansu.
“Kowa ya san arewa tana da arzikin ma’adanai masu daraja, shi ya sa da ake son sacewa sai aka kitsa mana kashe-kashe da sace-sace, kuma abin takaici ba mu da shugabanni nagari da za hana. Shi ya sa a kullum yankin komawa baya yake yi, muna sake kira ga jami’an tsaro da su guji harka da ‘yan siyasa domin amana ce suka ɗauka ta kare al’umma ba wasu tsirarun miyagun mutane ba kawai kuma za su yi wa Allah bayani saboda tsakani da talakawan arewa na cikin mawuyacin hali.” In ji shugaban gamayyar.
Ƙungiyar ta ce abubuwan da ake yi na rashin kishin ƙasa daga shugabanni ya ƙara sabbaba yunwa, matsalar tsaro da sauran ƙuncin rayuwa, ga kuma abin kunya harkar ilimi ta zama wasa da cin zarafin malaman jami’o’i.
“Yara matasa ‘yan label 400 (ajin ƙarshe) an ɓata musu karatunsu, wasu suna lokacin jarabawa aka rufe jami’o’i, ya kamata shuganinmu nagari su sake jajircewa kuma su ji tsoron Allah su ci gaba da faɗa wa juna gaskiya domin akwai ranar hisabi, abun dubawa a nan a yankin Yarabawa irin waɗannan halayen babu su, haka a yankin Inyamurai, duk inda ka bi mu ‘yan arewa ake kashewa, kuma hakan na ta faruwa tun daga kisan kisan gillar da aka yi wa manyan magabatanmu irin su Sardauna da Tafawa ɓalewa, don haka ya kamata wannan ya zama izina ga duk mai kishin ƙasa.” In ji Galadanci.