Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya rantsar da Honarabul Bala Aliyu Gusau a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara (ZASIEC) a wani ɓangare na shirye-shiryen gwamnatinsa gabanin zaɓen ƙananan hukumomi.
An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Litinin a yayin taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa wa’adin manyan shugabannin riƙo na ƙananan hukumin su 14 zai ƙare ne a ranar 23 ga Oktoba, 2024.
Sanarwar ta ƙara da cewa, babbar Alƙalin jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu, wacce Mai Shari’a Mukhtar Yusha’u ya wakilta ta rantsar da Shugaban Hukumar Zaɓen.
Har ila yau, Gwamna Lawal ya sanar da mambobin majalisar zartarwar jihar yayin zamanta cewa halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 da ya yi na da matuƙar amfani.
Ya bayyana fatan hakan zai haifar da sakamako mai kyau a ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar al’ummar Zamfara.
Gwamnan ya ce, ya sanya hannu kan gyaran dokar zaɓe ta jihar Zamfara makwannin da suka gabata gabanin zaɓen ƙananan hukumomin da ke tafe.
Ya ce, “A bisa hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a kwanan baya game da zaben ƙananan hukumomi, muna buƙatar mu gudanar da zabe a ƙananan hukumomin mu cikin aminci.
“A bisa ga rattaba hannu kan dokar da aka yi wa kwaskwarima, hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar za ta sanar da jadawalin zaben da wuri-wuri domin mu samu zababbun shugabannin ƙananan hukumomi a Jihar Zamfara.
“Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara (ZASIEC) za ta fito da tsare-tsare kan zaɓen, kuma ana sa ran dukkanmu za mu ba da goyon baya da haɗin kan da ya dace domin samun nasarar aikin.”
Bugu da ƙari, a yayin taron majalisar, Gwamna Lawal ya umurci Sakataren gwamnatin jiha da ya haɗa hannu da mataimakin gwamnan domin gaggauta shirya bikin ƙaddamar da Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Jihar Zamfara (ZIPA) domin ta yi aiki yadda ya kamata.
Gwamnan ya kuma sanar da majalisar cewa jihar a shirye take ta fara aikin rabon kuɗi na ‘NG-Cares’.
“Aikin zai ttallafa wa marasa galihu, matasa marasa aikin yi da mata a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar. Za a kashe jimillar kuɗi kusan Naira Biliyan 4.9.
“Masu cin gajiyar wannan shiri za su kasance mutane 5000 na matalauta da marasa galihu; ɗaukar matasa da mata marasa aikin yi 6000; tallafin inganta rayuwa rayuwa ga matasa da mata 8000.
“Dole ne mu yi adalci da nuna jagoranci nagari ga dukkan al’ummar jiharmu,” in ji shi