Wasu magoya bayan Jam’iyyar NNPP a Jihar Neja, sun yi watsi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin jagoran jam’iyyar.
Shugaban tsagin magoya bayan, Dokta Gilbert Agbo ne ya jagoranci zanga-zangar adawa da Kwankwaso a hedikwatar jam’iyyar da ke Minna.
- Gwamnatin Kano Za Ta Gyara Cibiyar Fasaha Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga
- Ban Ji Dadin Abin Da Libya Ta Yi Wa Super Eagles Ba – Tinubu
Ya ce Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya na barazana ga cigaban jam’iyyar.
Yayin taron Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Minna, Dokta Agbo ya jaddada cewa dakatar da Kwankwaso da Kwamitin Gudanarwa na Kasa ya yi a Legas, zai kawo karshen tasirinsa a jam’iyyar.
Don adawa da Kwankwaso, Dokta Agbo da mutanensa sun kone jar hula a hedikwatar jam’iyyar da ke jihar.
Kazalika, ya ce gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, yana da damar gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar saboda rashin bin dokokin jam’iyyar.
Sai dai a martaninsa, jagoran darikar Kwankwasiyya a Jihar Neja, Malam Danladi Umar Abdulhamid, ya bayyana shugabancin Dokta Agbo a matsayin haramtacce.
Ya ce zanga-zangar ba ta da alaka da jam’iyyar, sai dai don radin kansa.
Abdulhamid, ya tabbatar da cewa Rabiu Musa Kwankwaso har yanzu shi ne jagoran jam’iyyar na ƙasa .
Rigimar da ake yi yanzu a NNPP yana haifar da damuwa kan haɗin kan ’ya’yan jami’yyar.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar da masu sha’awar siyasar Najeriya na jiran su ga abin da zai faru a nan gaba.