Majalisar dokokin Jihar Jigawa, ta amince da kudurin dokar samar da wutar lantarki na shekarar 2024 don inganta wutar lantarki da rarraba ta ga al’ummar jihar.
Hakan ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar kan makamashi da ɗan majalisar mai shugabantar kwamitin, Muhammad Adamu daga Kafin Hausa, ya gabatar yayin zaman majalisar.
Ya ce Gwamna Umar Namadi ne ya aiko da kudurin don tantancewa da kuma da duba yiwuwar amincewa da ita.
Adamu, ya ce ƙudurin dokar wani bangare ne na Kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, inda aka bai wa majalisun dokokin jihohi damar kafa dokar sanar da wutar lantarki don amfanar da jihohinsu.
Dan majalisar ya bayyana cewa, hukumar ta nazarci dokar a tsanake tare da duba tsarinta da kuma amfaninta a ɓangaren wutar lantarki na samar da ababen more rayuwa da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar baki daya.
A cewarsa, zartar da kudirin dokar ya samu sahalewa, zai bayar da damar kafa hukumar samar da wutar lantarki ta Jihar Jigawa don inganta kasuwancin wutar lantarki.
Ya kuma tabbatar da cewa dokar za ta kuma kare mazauna jihar da masu zuba jari a fannin makamashi, wanda tuni an yi kowa tanadin da zai ci gajiyar ƙudirin kama daga masu zuba jari zuwa ga msu amfana da wutar.