A gabannin taron kolin shugabannin kasashe mambobin kungiyar BRICS na shekarar 2024, kafar CGTN ta CMG wato babban rukunin gidajen rediyo da talebijin na kasar Sin, ta shirya taron dandalin masana daga kasashe mambobin rukunin “Global South” wato kasashe masu tasowa da masu samun saurin bunkasuwa. Taken dandalin shi ne, “Zaman lafiya da ci gaba da tsaro: A hada kai domin gina duniya mai wadata”. Taron ya gudana ne jiya Laraba, karkashin jagorancin ma’aikatar kula da cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na JKS da CMG, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda aka samu mahalartar na zahiri ko ta kafar bidiyo, da suka hada da manyan jami’an gwamnatoci, da masanan da abin ya shafa, da wakilan kafofin watsa labarai daga kasashe 76 dake fadin duniya.
Ministan ma’aikatar kula da cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na JKS Liu Jianchao, da mataimakin ministan ma’aikatar yada manufofin JKS kuma shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo, inda Liu Jianchao ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, kuma za ta ci gaba da hada kai da sauran kasashe masu tasowa domin ingiza gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya yadda ya kamata.
- Xi Ya Amsa Wasikar Wakilan Daliban Da Suka Halarci Gasar Kere-Keren Kimiyya Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin
- Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Nijeriya Da ‘Yan Kwadago Sun Tashi Taro Babu Matsaya
A nasa bangare kuma, Shen Haixiong ya yi tsokaci cewa, babban rukunin CMG zai kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa, kuma zai yi kokarin samar da dandalin yada labarai da zai ingiza hadin gwiwa domin samun ci gaba tare, da tabbatar da adalci bisa bukatun masanan kasashe mambobin rukunin “Global South”.
Rahotanni sun ruwaito cewa, za a gabatar da shiri na musamman game da taron dandalin a kafar CGTN a gobe Juma’a 18 ga wannan wata. (Mai fassara: Jamila)