Gurasa dai wani nau’in abinci ne da ake sarrafa ta da fulawa ko kuma Alkama kamar kwatankwacin yadda ake sarrafa Burodi, amma da akwai wasu bambamce bambamce.
A Nijeriya, sana’ar sayar wa da kuma sarrfa Gurasa ta fi tasiri a birnin Kano, wanda ya kasance cibiyar Kasuwancin Nijeriya da yammacin Afrika.
- Gudunmawar Da Sin Take Bayarwa Wajen Tabbatar Da Wadatar Abinci A Duniya
- Ronaldo Da Messi Ne Kan Gaba A Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Albashi
A yanzu da abubuwa suka canja, masu sayar da gurasar na daukarta a faranti yayin da suke yawo da ita sako da lungu na cikin birnin Kano, kmar kasuwanni, ofisoshin gwamnati, tashoshin mota ko kuma kafa wata rufa ko wani waje domin siyarwa baya da yadda masu sana’ar siyar da nama su ma suke hadawa a wajajen sana’arsu.
Yawancin masu sarrafa gurasa sun kasance mata ne da suke zauna a gidajensu, yayin da masu sayarwa ke zuwa su sara bayan sun sarrafa ta.
Wata mai sana’ar sayar da gurasa ta sheda wa wakiliyarmu yadda ake hada gurasa da kuma abubuwan da ake tanada domin hada gurasar.
Mai sana’ar Gurasa: da farko ana auna yawan ko kuma adadin yadda ake son a yi Gurasar, ma’ana kamar yawan ya ake so ta kasance?
Mai sana’ar Gurasa: Sannan za a nemi babban mazubi domin ganin an zuba wannan adadin fulawar da ake bukata domin yin gurasar
Mai sana’ar Gurasa: Idan an zuba fulawa ana nemo yis da hoda sai a gauraya, sannan kuma sai a zuba ruwa daidai misali a ringa juyawa har sai ta hada jikinta
Mai sana’ar Gurasa: Baya ga haka kuma muna zuwa mu share Tanderu (inda ake gasa ta) sannan mu hada wuta da kara ko kuma karmami ko kuma gayen goruba wanda zai sa Tanderun yayi zafi.
Bayan yayi zafi muna debe wutar sannan sai mu ringa yanko curin kulin da muka hada sannan mu ringa danawa a jikin Tanderun. A haka muke yi har sai ta gasu.
Wasu na amfani da babban Tanderu domin yin gurasar da yawa a lokaci guda, yayin da wasu kuma suke amfani da kanana domin yin ta kadan.
Bayan ta gasu muna amfani da faranti domin kakabe ta, domin sake dana wata a ciki.
Gurasa dai ana sarrafata wajen ci ta hanyoyi da yawa, yayin da wasu ke sarrafa ta da garin kuli-kuli da mai. Wasu kuwa suna sarrafata da miya kala-kala.
Sakamakon dumamar yanayi da kuma barazabar amfani da wuta koda yaushe, wasu matasa sun yi hubbasar samar da hanoyin sarrafa gurasa da gasa ta a zamanance domin saukakawa masu sana’ar gudanr da aiyukansu.