Yadda Rashin Tarbiyya ‘Ya’ya Mata Ke Sanadiyar Jinkirin Aurensu, Ko Me Zakuce A Kan Hakan? Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakolo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacimmu na yau zai yi duba ne game da jinkirin auren ‘ya’ya mata a wannan zamanin.
- Yawan Karuwar GDPn Sin Daga Watan Janairu Zuwa Satumban Bana Ya Kai 4.8% Bisa Na Makamancin Lokacin A Bara
- Ronaldo Da Messi Ne Kan Gaba A Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Albashi
Bilkisu Maharazu
Assalamu alaikum. Agaskiya matsalolin da ake samu dangane da rashin tarbiyya da yake shafar ‘ya’ya mata sun hada da rashin kwabar su tun suna kanana domin shi ice tun yana danye ake tankwara shi in ya bushe ba ya tankwaruwa, yana da kyau tun yarinya tana karama a bata tarbiyya mai kyau yadda idan ta girma za ta tashi da ita ba tare da an samu tangarda ba, domin ‘yan magana suna cewa tarbiyya daga gida take faraway. Wasu mazaje suna lura da tarbiyyar mace kafin su aure ta kamar yadda shari’a ta ce ka nema wa ‘ya’anka uwa ta gari, Allah ya sa mu dace.
Rukayya Habibu
Hakika lamarin rashin tarbiyya ba karamin cikas yake kawo ba musamman ma idan maganar neman aure ta taso, wannan lamarin ba wai ya tsaya ne akan ‘ya’ya mata ba har ma maza, duk da yake dai abin ya fin illa ga su ’ya’ya mata saboda duk dadewa da za su yi wata rana sai sun samu masu aurensu.
Duk da yake dai daga karshe su ‘ya’ya mata aurensu za a yi, kowace kuma yadda halinta yake zai nuna irin yadda lamarin zaman aure zai kasance. Ko ba magana lalle kowa ya san tarbiyya tagari na jawo hankali musamman ma a ce a gida iyaye sun taka muhimmiyar rawa wajen ba da gudunmawa dangane da tarbiyya, saboda sanin kowa ne ice tun yana karami ake tankwara shi, in ya riga ya girma kuma, abin za iyi wuya manufa ana iya haduwa da matsala.
Malam Dauda Argungu mazaunin Mararraba
Ai dama duk inda ruwa ya je ya dawo kwari zai zauna, irin dabi’un Iyyaye suna taka rawa wajen yadda tarbiyyar ‘ya’yansu take kasancewa, saboda su duk abin da ‘ya’ya suka gani daga wurin iyayensu abin da tunaninsu zai basu ai masu kyau ne, don haka za su yi kokarin yin koyi da su. Shi ya sa akwai bukatar sa ido wajen lura da yadda tarbiyyar ‘ya’ya take ba ma kamar mata su komai dadewa gidan wani ne za su je.
Wasu ‘ya’yan ba laifinsu bane domin ai ana ganinsu saboda zama tare da su, da zarar an ga suna neman kauce hanya sai a maido su wadda ya dace su bi.
Habiba Tijjani
A gaskiya rashin tarbiyyar ba karamar taka rawa yake ba wajen sanadiyyar aure saboda za ki ga koda tafiya ta yi nisa tsakanin ma’aurata wato sun shaku da junansu musamman ma idan aka ce saurayi da budurwa ne to idan ya kai maganar gidansu abin da za’a fara tambayarsa shi ne ya tarbiyyar ta ta take ka binciki tarbiyyarta idan ya amsa musu to fa ba za su tsaya ga maganarsa ba sai suma sun yi nasu binciken iya bincike, sannan binciken da za su yi ba wai iya yarinyar kadai ba a’a babban abin da za su fara bincike a kai shi ne, da farko gidansu ya iyayenta su suma ya tarbiyyar su take, to daga nan ne za a iya kano iyayen suna da cikakkiyar tarbiyyar da har za su iya auren diyarsu?
Sai kuma a koma kan ita yarimyar, shin tarbiyyar da iyayenta suka ba ta tana amfani da ita ko kuma idan ta fita tana daukar wadansu daban, nan ma sai a yi bincike ya mu’amalarta take a waje, yarinya ce mai mutunci, mai da’a da sanin darajar mutane, shin ta iya girmama mutane, ta san girman na gaba da ita? Duk wannan sai an san su da zarar an samu akasin daya daga cikin wadannan sai ki ga amfara samun matsaloli ana bashi shawara idan kuma shima gidansu tsayayyu, ne sai ki ji suna cewa wannan auran ba zai yiyu ba ya canja wata to kin ga rashin tarbiyyar gaskiya ba karamar illa bace ga rayuwar ‘ya mace. Allah ya sa mu dace.
Usman Sani
Gaskiya yanzu lalacewa tarbiyyar ya tabarbare a wannan zamani wasu rashin tarbiyya tana farawa ne run daga gida, kuma ba wai iyayen ne ba su da tarbiyya ba a’a sun yaran ne yake kawo iyayen ba sa iya ba su kyakkyawar tarbiyya, saboda suna gudun bacin ran yaran shi ya sa iyayen ba za su iya dora su akan turba mai kyau ba sai dai a shagwaba su to kin ga ba kowanne namiji ne zai dauki komai ba za ki ga iyaye suna da tarbiyyar amma yaran sai yadda suke so haka za a yi.
To a gaskiya ya kamata mu rage nuna wa yara so da yawa saboda ya bamu damar nuna musu turbar da take daidai da wadda ba daidai ba mu kuma hada da addu’a.