Gwamnatin jihar Kebbi ta ɗauki matakin gaggawa don magance zargin satar kuɗi asusun marayun jihar, kimanin naira biliyan 2.1 da ƙungiyar Musulmi ta bayar don raba wa marayu 1,849 a jihar.
Wani taron manema labarai a Birnin Kebbi da Kwamishinan Harkokin Addinai, Alhaji Muhammad Sani Aliyu, ya gabatar, ya bayyana cewa Gwamna Nasir Idris ya bayar da umarnin a kwato kuɗaɗen cikin gaggawa kuma kwamitin zai binciki kan yadda aka yi amfani da na’urar cirar kuɗaɗe ta (POS) wajen badaƙalar.
- Bikin Ranar Sikila: Yara 138,000 Ake Haihuwa Da Cutar A Duk Shekara –Dr. Kangiwa
- An Yi Wa Matashi Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Yi Wa Yarinya Fyade A Kebbi
Kwamishinan ya ce duk bankin da aka samu da hannu za a ɗauki mataki a kansa. Ya kuma miƙa godiya ga kungiyar musulmi ta duniya bisa wannan karamci da suka nuna, ya kuma bayyana cewa ofishin yankin na kasa da ke Kaduna ya yi alkawarin bayar da haɗin kai wajen kwato kuɗaɗen.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin kwamishinan harkokin addinai ya ƙunshi wasu kwamishinoni biyu da masu ba da shawara na musamman da wasu manyan sakatarorin ma’aikatun jihar biyu, don ƙwato kuɗaɗen don mayar da su ga wadanda suka cancanta a jihar.