Tsohon dan majalisa, Farouk Lawan, ya fito daga gidan yarin Kuje a da ke Abuja, bayan ya cika wa’adin hukuncin daurin shekaru biyar da aka masa kan karbar rashawa.Â
Lawan, wanda ya jagoranci kwamitin binciken almundahanar tallafin fetur a Nijeriya, an same shi da laifin karbar rashawar dala $500,000 daga attajirin nan, Femi Otedola a shekarar 2021.
- Yaya BRICS Za Ta Kara Taka Rawa Wajen Ingiza Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Sun Sace Wasu A Neja
Shari’ar ta samo asali ne daga zargin neman cin hancin dala miliyan uku da ya yi domin cire wani kamfani daga jerin kamfanonin da ake bincike a kansu.
Shaidu da aka yi amfani da su a shari’ar sun hada da faifan bidiyo da ke nuna yadda Lawan ke karbar kudi, yana sunkumawa a babbar riga.
Da farko an yanke masa hukuncin shekaru bakwai, amma kotun daukaka kara ta rage masa zuwa shekaru biyar.
Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin a farkon shekarar 2024.
Bayan fitowarsa daga gidan yari, Lawan ya gode wa Allah, iyalansa, da abokan arziki da suka tsaya masa a lokacin da yake tsare.
Ya bayyana fitiwarsa a matsayin sabon babi a rayuwarsa, inda ya gode wa wadanda suka kasance tare da shi a lokacin da yake cikin matsin rayuwa.