Kwanaki kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bukata ga wanda yake so ya gaje shi a zabukan fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, an ga gwamnonin jam’iyyar mai mulki sun fara tururuwa zuwa wajen mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ake ganin shi ya dace da ra’ayin Shugaba Buhari.
An ga Gwamnonin jam’iyyar APC da dama a fadar shugaban kasa suna ganawa da Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, wanda hakan ake kyautata zaton goyon Bayan su ne na amincewa da Osinbajo a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Rahotanni sun ce gwamnonin da aka gani a Villa tsakanin Laraba zuwa Juma’a sun hada da na Kano da Ogun da Ekiti da Gombe da Nasarawa da kuma Ebonyi.
Rahotannin sun ce da alama mafi yawancin gwamnoni 22 da ke karkashin jam’iyya mai mulki sun amince da goyon bayan takarar Osinbajo, gabanin zaben fidda gwani da za a gudanar a ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin jihar Borno da Kaduna da Kano da Nasarawa da kuma Gombe suna adawa da dan takarar shugaban kasa da ya fito daga Yankin Arewacin Nijeriya a karkashin jam’iyyar APC.