An samu rudani kan ayyukkan hadakar kwamitin ma’aikatu da gwamnatin tarayya ta kafa domin aiwatar da hukuncin da kotun koli wacce ta yanke na bai wa kananan hukumomi 774 ‘yancin cin gashin kansu.
Wasu shugabannin kungiyar kananan hukumomin Nijeriya (ALGON), sun ce suna jiran hadakar kwamitin ma’aikatun ya bayyana samfurin yadda za a aiwatar da shirin.
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
- Me Najeriya Za Ta Iya Samu Daga Tsarin BRICS?
Kafa kwamitin mai mutum 10 tare da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya biyo bayan umarnin kotun koli na cewa kwamitin rarraba assun gwamnatin tarayya (FAAC) ya bayar da kudaden kai tsaye ga kananan hukumomin.
Kotun kolin ta kuma bayyana cewa ya saba wa tsarin mulki gwamnonin jihohi su rike kudaden da aka ware don gudanar da ayyukan kananan hukumomi.
Yayin da gwamnati ta yi gum kan wa’adin da aka bai wa kwamitin na gudanar da aikinsa, ana sa ran gwamnati tarayya za ta gaggauta daukar mataki kan wa’adin tun da kotun koli ta ba da umarnin daukar matakin gaggawa kan bai wa kananan hukumomin ‘yancin cin gashin kansu.
Wasu shugabannin kungiyar ta ALGON, sun shaida wa manema labarai cewa mambobin kungiyar sun damu kan jinkirin da kwamitin ke yi na kammala aikin da aka dora masa domin zartar da hukunci kotun koli.
Shugabannin kungiyan sun ce sun dauki matakan da suka dace don shirya taron manema labarai da zarar kwamitin ya bayyana shawararsa.
Rahotannin sun nuna cewa za a fara aiwatar da shirin ne a farkon watan Oktoba, yayin da gwamnatocin jihohi suka yi yunkurin shirya zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli domin cika tafarkin dimokuradiyya.
Jihohin Kaduna, Ribas, Bauchi, Benuwai, Imo, Kwara, Filato, Inugu, Abiya, Ebonyi, Kebbi, Sakkwoto da Akwa Ibom na daga cikin jihohin da suka yi zababbun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli.
Jihohin Katsina da Kano da Ogun da Osun da kuma Anambra suna cikin jerin jahohin da su ma ke shirin gudanar da zaben kananan hukumomi.
A ranar 24 ga watan Agusta ne aka kaddamar da mambobin hadakar kwamitin ma’aikatun domin aiwatar da hukuncin kotun koli wadada sun hada da SGF, Sanata George Akume a matsayin shugaba; ministan kudi; babban lauyan gwamnatin tarayya; ministan kasafi da tsare-tsare tattalin arziki; akanta janar na tarayya; gwamnan Babban Bankin Nijeriya; babban sakataren ma’aikatar kudi ta tarayya; shugaban hukumar rarraba kudaden haraji na kasa; wakilin gwamnonin jihohi da kuma wakilin kananan hukumomi.
Babban aikin kwamitin a cewar ofishin SGF shi ne, tabbatar da cewa an bai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu, ta yadda za su yi aiki yadda ya kamata ba tare da tsangwama daga gwamnatocin jihohi ba.
Ya kara da cewa matakin ya yi daidai da kokarin Shugaban kasa Bola Tinubu na ganin an aiwatar da tsarin da ya dace a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, wanda ya amince da kananan hukumomi a matsayin mataki na uku na gwamnati.
Gwamnatin tarayya ta bakin ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi ta maka jihohi 36 a gaban kotu bisa zarginsu da amfani da kudaden da aka ware wa kananan hukumomin a cikin asusun hadin gwiwa na jihohi da na kananan hukumomi.
A bisa dalilan da hukumomin tarayya suka gabatar tare da shaidu, kotun a hukuncin da ta yanke ta bayyana cewa ba bisa ka’ida ba ne gwamnonin jihohi su rike amfani da kudaden kananan hukumomi.
A kwanakin baya, ministan shari’a ya yi kira ga manyan lauyoyin kasar nan da su shawarci gwamnonin jihohi da su yi biyayya ga hukuncin da kotun koli ta yanke game da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi a Nijeriya.
Fagbemi, a wani taro da aka gudanar a Abuja, ya kuma gargadi shugabannin kananan hukumomin da su yi amfani da kudaden da aka ware masu ta hanyar da ta dace domin su ba gwamnonin jihohinsu ba ne za a tuhuma idan suka gaza.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakin ne wajen tafiyar da kananan hukumomin ta hannun shugabannisu sabanin gwamnoni.
A jawabinsa na bikin murnar cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba, Shugaba Bola Tinubu ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta aiwatar da hukuncin da kotun kolin ta yanke wanda ta ba da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi 774 na kasar nan a matsayin wani bangare na matakan da za a dauka domin inganta tattalin arziki.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan gwamnatin tarayya wajen aiwatar da hukuncin kotun koli na bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai.