Kwanan baya, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar JKS, kana shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin soja na JKS Xi Jinping ya amsa wasikar da dalibai da malaman jami’ar koyar da ilmin teku suka mika masa, inda ya taya su murnar cika shekaru 100 da kafuwar jami’ar.
A cikin sakonsa, Xi ya jadadda cewa, yana fatan za su yi amfani da damammaki masu kyau na wannan muhimmiyar rana, don kyautata tsarin darasi da fannonin karatu da na horar da kwararru bisa bukatun raya kimiyya da fasaha da tsare-tsaren kasa, da kuma kokarin horar da karin kwararru masu sha’awar ilmin teku dake iya sauke nauyin dake wuyansu a wannan fanni, ta hanyar kara yin kirkire-kirkire da ba da jagoranci ga kimiyya da fasahar ilmin teku.
Kwanan baya ne, dalibai da malaman jami’ar koyar da ilmin teku suka rubuta wata wasika ga Xi Jinping, don yi masa bayyani kan kokarin da suke yi a cikin shekarun karni da suka gabata, da kuma bayyana niyyarsu ta bautawa kasar wajen raya harkokin tekun kasar da samun ingantattun bunkasuwar kasar, har ma da taka rawa gwargwadon iyakacin kokarinsu wajen gaggauta raya kasar a duk fannoni da farfado da al’ummar Sinawa. (Amina Xu)