Akasari, an fi so manomi ya shuka Wake a watan Okutoba a Kudancin wannan kasa, inda kuma a Arewacin Nijeriya aka fi so a shuka Waken a watan Agusta.
Gyaran Gona:
Wanda zai noma Wake, idan bai mallaki gona tasa ta kansa ba; zai iya hayar wata gonar, musamman ganin cewa a cikin kwanaki kadan zai iya girbe shi, idan manomi yana da Naira 20,000; zai iya karbar gona haya, amma ya danganta da irin wajen da gonar take.
- Sin Ba Za Ta Canza Matsayarta Game Da Mayar Da Hankali Kan Kasashe Masu Tasowa Ba
- CBN Ya Ƙi Amince Wa Da Umarnin Majalisa Kan Dakatar Da Amfani Da Tsofaffin Naira
Har ila yau, ba a so manomi ya sake shuka Wake a gonar da ya noma shi, har sai bayan tsawon shekara uku, haka a kowace irin kasar noma; ana iya shuka shi.
Lokacin Shuka Shi:
Ana bukatar manomi idan ya tashi shuka Wake, ya shuka shi a ramin da zurfinsa ya kai daga mita daya zuwa mita biyu, inda kuma ake bukatar a kowane rami daya; a shuka Irinsa guda uku. Haka nan, ana so a bayar da sararin da ya kai daga mita 24 zuwa mita 30 a kowane layi guda, sannan kuma; Wake na fara rubawa ne a cikin kasar noma bayan kwana shida da shuka shi.
Ban Ruwa:
Waken da aka shuka na saurin rubawa a cikin kasar noman da aka shuka shi, haka nan yana iya girma ko da ba a yi masa ban ruwa ba, kazalika; Wake na bukatar ruwan saman da ya kai kimanin kwana talatin ana yin sa a jere.
Har ila yau, Irin nomansa bai cika bukatar ruwa sosai ba, domin ruwan zai iya kashe shi ta hanyar rubewar saiwowinsa, sai dai idan ruwan sama ya tsaya baki-daya, ana bukatar a yi masa ban ruwa, kazalika ba a bukatar manominsa ya rika yi masa ban ruwa a kan ganyensa; domin zai iya lalacewa.
Zuba Taki:
Ana bukatar manomin Wake ya yi amfani da takin gargajiya, musamman idan kasar noman da aka shuka shi ba ta dauke da wasu sinadarai, musamman don kara wa kasar noman inganci, har ila yau, manomi zai kuma iya zuba masa takin zamani.
Ba Shi Kariya Daga Kamuwa Daga Cututtuka Ko Kwari:
Ana bukatar manomi ya tabbatar da kare shi daga kamuwa daga kwayoyin cuta da kuma kwarin da ke yi masa illa, musamman don kauce wa tabka asara.
Lokacin Girbe Shi:
Akasari, Wake na kammala nuna ne a cikin kwana 80 ko kuma sama da haka, ya danganta da irin nau’in Irin da aka shuka; haka nan kuma ba a so a bata lokaci wajen girbe shi.
Kasuwancinsa:
Za ka iya sayar wa da mata ko mazan da ke yin sana’arsa, haka zalika; za ka iya sayar da akasarinsa a manyan shaguna ko kuma ga manyan diloli, sannan kuma za ka iya yin tallansa a kafar yanar Gizo ko fitar da shi zuwa kasashen waje da sauran su, inda a a baya; farashin buhu daya na Waken ke kai wa kimanin Naira 70,000.