Fannin noman Kabeji, abu ne sananne a dukkanin fadin wannan kasa da muke ciki, musamman sakamakon yakinin da wasu ke da shi na cewa; ya fi yin kyau idan aka shuka shi a Jihar Filato, amma a hankali sauran wasu manoma a nan Nijeriya; su ma suka rungumi nomansa.
Har ila yau, akwai wasu daidaikun mutane da ke noman sa a Kudu Maso Yammacin wannan kasa, haka zalika za a iya noman sa a kowane yanki da muke da a fadin wannan kasa.
- Sin Ba Za Ta Canza Matsayarta Game Da Mayar Da Hankali Kan Kasashe Masu Tasowa Ba
- Gwamnatin Tarayya Da Google Sun Bullo Da Hanyar Samar Wa Da Matasa 2,500 Aikin Dogaro Da Kai
Kabeji ya fi saurin girma a ma’aunin yanayin da ya kai daga 55 zuwa 60, inda kuma akwai nau’ikansa da ke saurin girma a ma’aunin yanayin da ya kai daga 20 zuwa 25.
Har wa yau, nomansa ya samo asali ne daga farkon kafuwar Kasar Girka da kuma Kasar Romaniya, inda nomansa ya ci gaba da yaduwa zuwa kasar Birtaniya, ya kuma ci gaba da yaduwa zuwa sauran wasu kasashe.
Akasari a Nahiyar Afirka, musaman a Nijeria; ana yawan yin amfani da shi a lokutan bukukuwan Sallah ko na Kiristimeti da sauransu, ya kuma kasance yana dauke da sinadarin ‘calcium da ke inganta lafiyar jikin Dan’adam.
Bugu da kari, nomansa ba shi da wata wahala; sannan kuma akwai sauki wajen kula da shi bayan an shuka shi. Haka nan kuma, ba sai kana da kudi mai yawa za ka iya fara yin nomansa ba, ko a bayan dakinka za ka iya noma shi.
Gyaran Gona:
Ana iya shuka shi a kan kowace irin kasar noma, kadai abin da ake bukata shi ne; bayan manomi ya gyara gona, sai ya shuka Irin da yake da shi. Haka nan, manomi zai iya amfani da motar Tarakta; don yin gyran gonarsa, musaman idan kasar noman na da tsauri sai ya yi mata haro; ya shuka Irinsa.
Shuka Shi:
Ramin da za ka shuka Irin nasa, ana so ya kai zurfin kimanin daga kafa biyu zuwa uku, idan kuma za ka yi renon Irin ne; ana so ka saka shi a cikin buhu ko kuma cikin ledar da ake yin renon Irin, daga nan bayan sati uku zuwa hudu sai ka canza masa wani gurin daban; bayan ya kai tsawon santi mita 14 zuwa 16.
Yi Masa Ban Ruwa:
Ana so a rika yi masa ban ruwa a kai a kai duk bayan sati guda, ganin cewa Kabeji na bukatar ruwan da ya kai santi mita 3.8, musamman ganin cewa; Kabeji ba ya son yanayi na fari.
Zuba Masa Taki:
Ana so tun farkon lokacin da aka shuka Irinsa, a zuba masa takin zamani, musamman don ya yi saurin girma; inda kuma bayan sati uku da canza masa wani gurin, ana so a kara zuba masa wani takin.
Kare Shi Daga Kamuwa Da Cututtuka:
Kamar sauran amfanin gona, shi ma Kabeji akwai cututtukan da ke yi masa illa; kamar irin wadanda ake kira a turance ‘flea beetles’, da sauran makamantansu.
Lokacin Girbe Shi:
Ana yi masa girbi bayan ya gama girma baki-daya, sai dai ya danganta da nau’in Irin da aka yi amfani da shi, haka nan bayan girbe shi, ana iya samun daga tan 70 zuwa 80.
Sayar Da Shi:
Manomin da ya noma shi, zai iya sayar da shi ga ‘yan kasuwar da ke yin sana’arsa ko a manyan shaguna da gidajen sayar da abinci ko a Otel ko kuma ya yi tallansa a kafar yanar Gizo.
Adana Shi:
Bayan an gibe shi, ana kuma bukatar a adana shi a wurin da yake da sanyi, za kuma a iya adana shi har zuwa wata uku.