Tsohon shugaban kasar Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana yadda ya fadi zaben shugaban kasa na 2015.
Ya bayyana cewa faduwa zaben na daga cikin lokutan da suka fi muni a rayuwarsa ta siyasa.
Jonathan ya yi takara a jam’iyyar PDP, inda ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya zama shugaban kasa na farko mai ci da ya gaza yin tazarc tarihin Nijeriya.
Jonathan ya bayyana cewa ya ji kamar duk duniya ta juya masa baya lokacin da aka sanar da sakamakon zaben.
Sai dai ya yaba wa Raymond Dokpesi, tsohon shugaban kamfanin Daar Communications, wanda ya goya masa baya.
Dokpesi ya karfafa masa guiwa tare da ba shi goyon baya.
Jonathan ya ce goyon bayan ba kawai ya taimaka masa wajen mika mulki ba ne, har ma ya shafi rayuwarsa.
Tsohon shugaban ya bayyana dalla-dalla yadda ya samu kansa a ciki a cikin littafinsa mai suna “My Transition Hours.”