Mai martaba Sarkin Ogbomosoland, Oba Alayeluwa Ghandi Afolabi Olaoye, Orumogege III, ya aika sakon taya murna ga Agba-akin na Ogbomoso, Hon. Sunday Dare, bisa naɗinsa a matsayin mai ba da shawara na musamman kan yaɗa labarai ga Shugaba Bola Tinubu.
Sarkin ya bayyana godiya ga Tinubu bisa wannan zaɓi, yana mai cewa zaɓin Dare ya nuna ƙudirin shugaban ƙasa na neman abokan aiki masu ƙwarewa. A cikin wata sanarwa da Oba Ghandi ya sa hannu, ya ce, “Muna godiya ga Shugaba Tinubu bisa yadda ya gane ƙwarewar Dare ta fannin aikin jarida.
- An Kaddamar Da Bikin Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Rasha a Kazan
- Tinubu Ya Yi Wa Majalisar Zartarwa Kwaskwarima
Ya ƙara da cewa, “Mutanen Ogbomosoland sun yi maraba da wannan naɗin, suna da tabbacin cewa ƙwarewar Dare zai taimaka wa gwamnatin Tinubu. A madadin mutanen Ogbomosoland, muna godiya ga Shugaba Tinubu tare da yi wa Hon. Sunday Dare fatan alheri a sabon aikinsa.”