Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sallami babban mai horar da kungiyar, Eric Ten Hag daga aiki, bayan shekara biyu kacal da fara aiki a Old Trafford.
Eric ya lashe kofuna biyu a Manchester United da su ka hada da Carabao Cup da kofin FA, a kakar wasa ta bana Ten Hag ya gamu da cikas bayan rashin nasara sau hudu canjaras 2 da nasara uku kacal.
Hakan ya sa mahukuntan kungiyar bayan wani zama da suka yi a Landan su ka yanke shawarar sallamarshi inda mataimakin kocin, Ruud Van Nistelrooy zai cigaba da jagorantar Man Utd kafin a samu sabon koci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp