Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa matatar man fetur dinsa tana da wadataccen mai da zai iya biyan bukatun Najeriya.
Amma ya ce dole ne ‘yan kasuwa su fara dakon mai daga matatarsa don rage karancin da ake fama da shi yanzu.
- ‘Yan Bindiga Sun Fara Mamaye Dajin Da Ake Horar Da Sojojin Nijeriya
- Kasar Sin Ta Yi Tir Da Dokokin Amurka Na Dakile Zuba Jari A Sassan Fasaha Na Sin
Ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa a ranar Talata.
Dangote, ya yi bayanin cewa matatarsa na iya samar da lita miliyan 30 na man fetur a kullum, kuma tana da wajen ajiye man fetur kimanin miliyan 500 a yanzu.
Ya jaddada cewa aikinsa shi ne samar da mai da siyarwa a babban mataki, ba ya sayarwa kai-tsaye ga gidajen mai ba.
‘Yan kasuwa na bukatar su fara dakon mai daga matatarsa domin tabbatar da cewa ya isa wajen mutanen da ke da bukata.
Dangote ya tabbatar wa jama’a cewa matatar tasa a shirye ta ke wajen biyan bukatarsu a bangaren man fetur.