Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), ta amince da Naira biliyan 2.6 don siyan motoci da na’urori ga jami’an tsaro da ke aiki a babban birnin tarayya, Abuja.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Muhammed Bello, ne ya bayyana haka a lokacin da suke zanta wa da manema labarai a fadar shugaban kasa kan sakamakon taron majalisar na yau Laraba.
- Ministar Jin Kai Ta Raba Wa Mata 3,500 Tallafin Kudi A Gombe
- Yajin Aikin ASUU: Kungiyar Dalubai Ta Bukaci A Kori Ministan Ilimi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron na yau Laraba a Abuja.
Bello, ya bayyana cewa majalisar ta amince da Naira biliyan 2.6 don siyan motocin aiki da na’urori ga hukumomin tsaro domin yakar aikata laifuka a daukacin kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce: “A yau, na gabatar da kudirin sayan motocin aiki, na’urorin tsaro da na’urorin da za su tallafa wa jami’an tsaro da ke aiki a babban birnin tarayya.
“Wadannan kayayyaki motocin amfani ne guda 60 da suka hada da na’urorin sadarwa da za a saka a cikin motocin, wadanda za a kawo su a kan kudi N1,835,108,613.95 tare da kawo su nan da watanni biyu.”
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin birnin tarayya ta kuma samu amincewar sayen karin kayayyakin aiki ga hukumomin tsaro da ke da alhakin tabbatar da tsaro a yankin.
Ayyukan ‘yan bindiga sun fara kamari a wasu yankuna na birnin tarayya, Abuja.
A satin da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari shingen wasu dakarun soji da kedutsen Zuma da ke yankin Madalla, daura da shiga Abuja.
A baya-bayan nan ‘yan bindiga sun yi barazanar kai hare-hare birnin tarayyar, lamarin da ya sanya rufe makarantu da wasu muhimman wurare.