Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nada Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin mukaddashin babban hafsan sojin kasa (COAS).
Oluyede zai yi aiki a kan mukamin har zuwa lokacin da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja zai dawo.
Talla
Kafin nadin nasa, Oluyede ya rike mukamin kwamandan runduna ta 56 na rundunar sojojin Nijeriya da ke Jaji, Kaduna.
Cikakken bayani na nan tafe…
Talla