Jama’a barkanmu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa.
A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Mukaddashin Editana Malam Bello Hamza, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro
Sako daga Auwal Muhammad:
Assalaikum alaikum!
Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na ina musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyayena da kannansu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a, ina gaida abokaina wadanda muka yi makaranta tare tun daga firamare, Sakandire, jami’a, abokan aikina duk ina mika sakon gaisuwata a gare ku da fatan kuna cikin koshin lafiya, Allah ya sa haka amin.
Sako daga Abbas Sambo
Ina mika sakon goron Juma’a ga al’ummar Musulmi gaba ki daya, da jamia’an tsaro da ke kasar nan baki daya tare da kokarinsu da fatan Allah ya taimake su ya ba su ikon jajircewa akan aikinsu. Ina mika gaisuwata ga mahaifiya ta Hajiya Asabe, da mahaifina Alhaji Sambo Lawan. Ina mika sakon gaisuwata ga yayata Firdausi, da kanwata Nusaiba, da yayana Mu’azu, da kanina Ibrahim, da yayana Ma’aruf. Da fatan sakona ya iso ku cikin koshi lafiya. Allah ya sa haka amin.
Sako daga Aisha Yusuf
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Safiyya Umar
Assalamu alaikum! Al’ummar Musulmi ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan mun yi Sallar Juma’a lafiya, alkhairin dake cikin wannan rana Allah ya sa da mu da shi, sharrin dake cikin wannan rana Allah ya kare mu da shi.
Ina mika sakon gaisuwata ga iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na nesa, duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana, Allah ya ba mu zaman lafiya a kasarmu amin.
Sako daga Uwaisu Adamu
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwata ga wannan gidan jarida mai albarka tare da mika kodiyata da suka bani dama da na mika sakon gaisuwata, na gode Allah ya albarkaci wannan gidan jarida.
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga iyaye na da fatan alkhairin a gare su Allah ya saka musu da alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwata ga ‘yan uwana, yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina gaida abokan arziki na kusa da na nesa, ina yi musa fatan alkhairi da fatan duk mun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya sa haka amin.