Hukumar raba kudaden shiga da hada-hadar kudi ta Nijeriya (RMAFC) ta koka kan tsadar harkokin mulki a Nijeriya tsawon shekaru, tana mai cewa Nijeriya ce mafi girma a yankin kudu da hamadar Saharan Afirka tafi kashe kudade wajen tafiyar da gwamnata.
Hukumar ta ce lamarin da ke da ban tsoro da rashin dorewa kan yadda jama’a ke nuna damuwa da tattaunawa saboda mummunan tasirinsa da ke janyo wa bangaren zuba jari, fadada masana’antu da samar da ababen more rayuwa, da kuma ci gaban hakikanin fannin tattalin arziki.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Manjo Janar Olufemi Muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa
Shugaban hukumar, Dakta Muhammad Bello, shi ne ya bayyana haka a Abuja, inda ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa umarnin da ya bayar na rage yawan ayarin ministoci da manyan jami’an gwamnatinsa a matsayin hanyar rage tsadar tafiyar da gwamnati, yayin da ya bukaci gwamnatocin jihohi su ma su yi koyi da shi.
Ya yi kira da a rage yawan masu rike da mukaman siyasa kamar yadda aka ba da shawarar a cikin kunshin biyan albashi na RMAFC, na masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati da kuma tabbatar da yadda ake kashe kudaden gwamnati a kowane mataki.
Shugaban RMAFC ya ce, “Shaidu sun nuna cewa Nijeriya ce kasa wacce aka fi kashe kudade wajen tafiyar da gwamnati a duk kasashen da suke Afirka. Hukumar ta fito fili ta bayyana matsayarta kan wannan batu ta hanyar gabatar da takarda.
“A bayyane yake cewa farashin mulkin Nijeriya yana daya daga cikin mafi girma a yankin kudu da hamadar Saharan Afirka, wanda ya kawo cikas ga gwamnati wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta kamar su raya ababen more rayuwa, samar da ingantaccen kiwon lafiya, inganta harkokin ilimi da dai sauransu.”
Dakta Shehu ya ce matakin zai taimaka matuka wajen rage tsadar harkokin mulki, wanda wani bangare ne ke da alhakkin rage samar da ababen more rayuwa da walwala da faduwar zuba jari da rashin aikin yi da karuwar rashin tsaro a kasar nan.
Ya kara da cewa babu wata al’umma da za ta iya samun ci gaba mai ma’ana, sai dai idan ta samar da ingantaccen tsarin tafiyar da al’amura gwamnati da za su iya amfani da albarkatun kasa domin amfanin kowa.
Ya ce hukumar RMAFC ta yi shekaru da yawa tana yaki da lamarin, ba wai kawai ta bayar da shawarar rage farashin mulki ba ne a matsayin hanyar tadanar kudade, sannan kuma ta ba da shawarwari masu yawa ga gwamnati a dukkan matakai kan tsarin bukatar rage yawan kashe kudin da ba dole ba da kuma lura da kashe kudi kan ayyukan ci gaba wadanda za su yi tasiri mai kyau ga rayuwar ‘yan kasa.
A cewarsa, tsadar harkokin mulki a Nijeriya ya samo asali ne sakamakon tsadar manyan ofisoshi, da yawan ma’aikatun da hukumomin gwamnati da kuma cin hanci da rashawa.
“Sauran abubuwan sun hada da tsadar ayyukan gwamnati sakamakon gazawar ababen more rayuwa, tsadar tsaro sakamakon ta da kayan baya, garkuwa da mutane da ta da kayan baya da kuma fashi da makami, yawan albashi da alawus alawus, almubazzaranci da ayyuka da kashe kudade, dimbin basussuka na gida da waje da kuma raunin cibiyoyin tilasta aiwatarwa da ayyuka,” in ji shi.