Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya nuna takaicinsa kan yadda hazikan matasan Nijeriya ke sulalewa su na ficewa daga cikin kasar zuwa kasashen ketare.
A cewar Jega, a irin wannan yanayin na tafiya zuwa wasu wurare domin gwagwarmayar neman rayuwa mai kyau, babban barazana ce ga fatan ci gaban kasar nan.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro
Da yake magana a wajen kaddamar da wata kungiya mai zaman kanta, mai rajin farfado da Nijeriya (URNI) a Abuja, Jega ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi duk mai yiwuwa wajen farfado da fatan ci gaban kasar nan.
Ya ce, “Yanayin gwagwarmayar kasar nan a halin yanzu, wanda ya kunshi har da yanayin talauci da ke addamar kasar da kuma karuwar ficewar matasa masu hazaka da aka fi sani da ‘Japa’ abun damuwa ne matuka gaya.
“Wannan yanayin babban barazana ce ga fatan ci gaba, dole ne masu kishin kasa su tashi tsaye wajen yin duk mai yiwuwa domin farfado da fata ga cikin kasar.”
Yayin da yake cewa lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai, lokaci ne da kasar ta zama fitilar bege ga dukkanin Afrika, wanda ya zaburar da al’ummomin da suka kasance bakaken fata a fadin duniya.
Jega ya jinjina wa shugabannin da suka sadaukar da kansu a jamhuriyya ta farko har aka samu nasarar da aka samu.
Ya kara da cewa, wadannan shugabannin masu kishi su ne suka aza tubalin ci gaban kasar nan da har yanzu ake kan mora.
Tsohon shugaban INEC ya nemi ‘yan Nijeriya da su shure kowace irin ikirari da ke nuni da cewa Nijeriya kasa mara ci gaba. Sai dai, ya nemi da a yi aiki tukuru domin gina kasa da cire kowace irin bambance-bambance domin al’umman kasar nan su more kasar.
A nasa jawabin, ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce, ‘yan Nijeriya sun cancanji rayuwa mai inganci fiye da a zauna a yi ta musu karin alkawura.
Ministan wanda ya samun wakilcin darakta janar na hukumar wayar da kai ta kasa, Lanre Isa Onilu, ya ce akwai bukatar alkawuran da aka yi wa ‘yan Nijeriya an cika su. Ya ce, “Domin tabbatar da azamarmu, dole ne mu tabbatar mun aiwatar da alkawuran da muka yi wa jama’anmu.”
Uban kungiyar URNI, Hassan Tukur, ya ce, matsalolin da suke akwai suna da nasaba da rashin shugabanci na kwarai, ya nemi a cire bambancin addini ko na kabilanci domin ganin rayuwa da kyautata da ingantuwa a kasar nan.