Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar II, ya bayyana cewar lamarin gararanbar almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta babbar kalubale ne da dole shugabannin arewa su tashi tsaye wajen dakilewa.
Sultan ya lura kan cewa miliyoyin yara ne ke gararanba a kan layuka, titina, kwararo-kwararo, kauyuka da birane a fadin kasar nan kowace rana.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro
Ya shaida hakan ne a lokacin da ke gabatar da jawabinsa a wajen taron kungiyar gwamnonin arewa da sarakuna da ya gudana a Jihar Kaduna ranar Litinin.
Ya nemi gwamnonin da su maida hankali kan wannan lamarin domin ganin sun tattauna yadda za a samu shawo kan matsalar, inda yake nuni da cewa, hakki ne da ke wuyansu da su shawo kan matsalolin da shiyyar ke fuskanta.
Sultan ya kara da cewa a matsayinsu na shugabanni, dole ne su mara wa sabuwar hukumar Almajiri da yaran da ba su zuwa makaranta a shiyyar domin tabbatar da an cimma nasarar kafa wannan hukumar don su.
“Muna da yara daruruwa, in ma ba dubbai ko miliyoyi ba da suke gararanba a kan layuka. Wannan hukumar dole ne mu mara mata baya domin ganin ta cimma nasarar shawo kan matsalar yaran da suke gararanba a kan titina. Muddin ka ilmantar da wani, ka samar masa da ‘yancinsa, domin yin aiki wa kansa da kuma al’umma.
“A shirye muke mu yi aiki tare da ku, kuma za ku iya samunmu a kowani lokaci. Inda kwarin guiwar da wannan hadin gwamnonin arewan da suka hada kai domin tabbatawa tabbas za a samu nasara.”