Wadannan matasa, masu shekaru 12 zuwa 15, sun shiga cikin zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi a Kano da sauran wurare a watan Agusta, inda suka yi magana kan korafin su ga gwamnatin.
Shari’ar, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Obiora Egwuatu, ta fara ne tare da sa su a kan kujerar masu laifi, amma daga baya wasu daga cikinsu suka yanke jiki, wanda ya sa aka dakatar da zaman na wucin gadi.
Lauyan masu kare su, Marshall Abubakar, ya bayyana cewa an tsare matasan tun ranar 3 ga Agusta, inda suke fuskantar yanayi mai tsanani da rashin kulawa da rashin abinci. Ya danganta faduwar nasu da yunwa da kuma rashin lafiya saboda tsawon lokacin da suka shafe a tsare.
- Gwamnatin Kano Za Ta Gyara Cibiyar Fasaha Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga
- Ɗaliban Kwalejin Kimiyya Ta Jega Sun Yi Zanga-Zanga Har Da Ƙone-Ƙone
Bayan wannan lamari, jami’an lafiya na kotu sun shigo domin ba da taimakon gaggawa ga matasan da suka yanke
jiki.