Saratu Garba, yarinya ‘yar shekara 11 da ba ta zuwa makaranta, ta samu tallafin karatu daga kungiyar ‘Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE), acikin wani shiri da bankin duniya ke tallafawa.
Ƙwararriyar yarinyar ta samu baiwa ne a bangaren Ilimin lissafi, an ya yada bidiyon Saratu kwanan nan a shafukan sada zumunta, anga yadda take wa lissafi watsa-watsa wanda hakan ya jawo hankulan mutane da yawa suka nuna kauna a gareta Sabida basirarta.
A ranar Laraba a Kano, Aliyu Yusuf, jami’in sadarwa na shirin AGILE, ya ce ofishin aikinsu na kasa ya umurci ofishinsu na Kano da ya nemo yarinyar sannan su dauki nauyin Karatunta.
Saratu Garba ta fito ne daga kauyen gwadahi dake masarautar Gaya a jihar Kano.
“A ziyarar da tawagar AGILE ta kai Majalisar Masarautar Gaya, sai aka gayyaci yarinyar da iyayenta zuwa fadar sarkin.
“Wakilan ma’aikatar ilimi ta jihar Kano da tawagar AGILE sun yi wa mai martaba sarki, Alhaji Ali Ibrahim-Abdulkadir bayanin aniyar aikin sauke nauyin karatun yarinyar,” inji shi.
Nan take, Wakilin ma’aikatar Ilimi, Haruna Muhammad-Panidau, ya mika kayan makaranta da jaka da sauran kayan karatu ga yarinyar mai hazaka.
Mai Tsare-tsare na ayyukan shirin AGILE a Kano, Ado Tafida-Zango, shi ma ya mika wa yarinyar Naira 20,000 domin tallafa wa karatun ta.
Saratu ta shaida wa wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, wanda ya ziyarci garinsu, kauyen Gwadahi a Gaya, Saratu ta shaida cewa ta fita makaranta ne a aji hudu na firamare ta koma tallace-tallace.
“Na kware a ilimin lissafi, ko kari, ragi, rarrabawa ko ninkawa. Zan iya lissafin lambobi a cikin miliyoyi a kwakwalwata, ba tare da na rubuta ba ko amfani da kalkuleta.
“Na bar makaranta ne saboda cin zarafin da ‘yan ajinmu ke min, sun kasance suna kirana da sunayen da ba na kauna.
“Ba zan koma waccan makarantar ba. Zan yi farin cikin ci gaba da karatu a wata makaranta, nesa da su,” in ji ta.