Shugaban kasar Finland Alexander Stubb, ya iso birnin Beijing a ranar 28 ga watan Oktoba da ya gabata, inda ya fara wata ziyarar aiki ta yini hudu a kasar Sin, kuma ya kawo ziyara ne a daidai lokacin zagayowar bikin cika shekaru 74 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Finland. Wannan kuma shi ne karo na farko da Alexander Stubb ya kawo ziyara kasar Sin, tun bayan da ya hau karagar mulkin kasar Finland.
Yayin zantawarsa da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, Stubb ya ce, har kullum ci gaban kasar Sin yana matukar ba shi mamaki, inda ya ce, ya taba ziyartar Shanghai, da Chengdu da sauran wasu birane da dama na kasar, kuma duk lokacin da ya zo, ya kan ganewa idanunsa sabon ci gaban kasar.
- Shugaba Xi Ya Gana Da Kantoman Yankin Musamman Na Macao Na Kasar Sin
- Senegal Ta Kulla Yarjejeniyar Gudanar Da Aikin Karkatar Da Ruwa Da Kamfanin Kasar Sin
Game da ma’anar wasu jerin muhimman shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya bullo da su ga ci gaban dukkanin fadin duniya kuwa, shugaba Stubb ya bayyana cewa, yanzu duniya na kunshe da bangarori daban-daban, kuma dole ne ra’ayin kasantuwar bangarori daban-daban a duniya ya zama tushe. In ba haka ba, za’a fada tashe-tashen hankali ko rashin zaman doka da oda.
Shugaban ya kara da cewa, ya zama dole a bada iko, musammnan ga kasashe masu tasowa, idan har ana son shawo kan wasu manyan kalubaloli da duniya ke fuskanta, ciki har da sauyin yanayi, da matsalar karuwar jama’a, da matsalar bakin haure, da ci gaban fasaha, da shawo kan cututtuka masu yaduwa, ko samar da ci gaba mai dorewa, ya zama dole sassan kasa da kasa su hada kai don neman mafita, saboda babu wata kasa da za ta iya magance su ita kadai.
Daga nan sai shugaba Stubb ya ce ya kamata a kiyaye ka’idojin yanzu, saboda suna kan turba mai kyau, amma duk da haka ana bukatar daidaita tsarin bada iko na yanzu, don kara baiwa kasashe masu tasowa iko. (Murtala Zhang)