Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana kantoman yankin musamman na Macao Sam Hou Fai, wanda aka zaba a baya bayan nan, kana gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta amince da nadin sa.
A jiya Juma’a ne shugaba Xi ya gana da Sam, a babban dakin taruwar jama’a dake nan birnin Beijing, zaman da firaministan kasar Li Qiang ya halarta, kuma a lokacin aka mikawa Sam takardar nadin sa a matsayin kantoman yankin musamman na Macao na 6.
- An Zargi FIFA Da Kin Biyan Hakkokin ‘Yan Wasa
- Rungumar Harkar Noma Mafita Ce Ga Ma’aikata Masu Ritaya
Shugaba Xi ya taya Sam murnar nadin sa, tare da jinjina masa game da yadda yake rike da akidar kaunar kasa, da ma yankin musamman na Macao, da yadda yake aiki tukuru wajen sauke nauyin dake wuyansa, da gudummawarsa ga samar da daidaito da bunkasar yankin Macao, a tsawon lokaci da ya yi yana rike da mukamin shugaban babbar kotun daukaka kara ta Macao.
Da yake maida jawabi, Sam ya bayyana matukar godiya da nada shi da aka yi a matsayin kantoman yankin musamman na Macao na 6, yana mai shan alwashin aiwatar da cikakke, kuma madaidaicin tsarin nan na “Kasa daya tsarin mulki 2”, da kare ikon mulkin kai, da tsaro da ci gaban moriyar kasa.
Kana da hade tsarin yankin Macao cikin babban tushen bunkasa kasar Sin, da gaggauta zaburar da ci gaban mabanbantan manufofin bunkasa tattalin arziki a fannoni daban daban na Macao. (Saminu Alhassan)