A yau 5 ga watan Nuwamba za a fafata tsakanin Kamala Harris da Donald Trump a zaben Amurka, wanda sakamakon zai ta’allaka ne a jihohi bakwai na kasar.
Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris da tsohon shugaban kasar, Donald Trump suna ci gaba da zage damtse a zaben mai cike da tarihi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Soke Kwangilar Gyaran Titin Abuja Zuwa Kaduna Da Kano
- Dole Ne A Gyara Kuskuren Da Tsirarrun Kasashe Suka Yi Na Kiyaye “Dangantakar Diflomasiyya” Tsakaninsu Da Yankin Taiwan
A muhimman jihohin da ke kan gaba a fafatawar ta 2024, ana iya cewa babu wata tazara sosai tsakanin abokan hamayyar biyu a zaben da ke gudana.
Jihohinn kasar guda 50 na da ‘yancin gudanar da zaben shugaban kasa.
A tsarin zaben Amurka , kowace jiha tana da adadin kuri’u na wakilain masu zabe bisa ga yawan al’ummarta.
Yawancin jihohi suna da tsarin karba-karba wanda ke bai wa duk wanda ya lashe zaben fidda gwani damar samun kuri’u.
A wannan shekara dai, za a fafata ne a muhimman jihohi guda bakwai, kuma kowane daga cikinsu yana da rawar da zai taka wajen samun nasara ko akasin haka.
Kamala Harris da Donald Trump, sun yi yakin neman zabe a jihohi daban-daban wanda suka yi ta jefan juna da munanan kalamai don nuna karfin adawar da ke tsakaninsu.
A irin wannan taro na yakin neman zabe ne aka kai wa tsohon shugaban kasar, Trump hari da bindiga, amma ya tsallake rijiya da baya.
Trump ya samu rauni a kunnensa bayan da jami’an tsaro suka yi gaggawar dauke sa zuwa waje mai tsaro.
Ita kuwa Harris ta samu damar tsayawa takara, biyo bayan matsin lambar da aka dinga yi wa Joe Biden na ajiye muradinsa na sake yin takara.
Wannan matsin lamba ya sanya shugaban na Amurka, ajiye burinsa na sake yin takara a karo na biyu, tare da zabar Harris a matsayin wadda za ta gaje shi.