Babban tashar samar da wutar lantarki ta ƙasa ta sake lalacewa, wanda ya bar yawancin ƴan Nijeriya a cikin duhu.
Wannan lamari ya faru ne da misalin ƙarfe 11:28 na safe a yau Alhamis, wanda sau biyu kenan a cikin makon nan kuma na goma a shekarar 2024.
- Katsewar Wutar Lantarki: Mun Yi Asarar Fiye Da Naira Biliyan 6 – KEDCO
- Da Ɗumi-ɗumi: DisCos Sun Sanar Da Sabbin Farashin Mitar Wutar Lantarki
Rahoton ISO, wani sashi na kamfanin rarraba da wutar lantarkin na Nijeriya (TCN), ya hanuna cewa dukkanin tashoshin samar da wutar da ke haɗe da babbar tashar ɗin ba su samar da wuta ba a tsakiyar yau ba rana, bayan sun samar da megawatt 2,323 da misalin ƙarfe 11 na safe.
Shafin yanar gizo na ISO ya nuna 0.00 MW da ƙarfe 12 na rana, wanda ke nuni da cikakken sauka gaba ɗaya.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos ya tabbatar da faruwar wannan lamari, yana mai danganta matsalar katsewar hasken ga rashin wuta daga Babbar tasha ta ƙasa.
“Rashin samar da wuta daga babbar tashar ɗin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:28 na safiyar yau, Alhamis, 7 ga Nuwamba, 2024, wanda ya jawo rashin wuta a duk ƙananan tashoshinmu,”
A Jos Disco, tare da bayar da tabbacin cewa ana ƙoƙarin dawo da wutar da zarar an kammala ɗin ya farfaɗo.