Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da tsarin yakar gurbatar yanayi da kuma yakar zubar da bolar robobi a daukacin fadin kasar.
Ta kuma yi fatan masu zuba hannun jari a kasar, za su zuba hannun jarinsu, a kan yadda za a rinka magance watsar da robobin ako ina a fadin kasar.
- Sin Da AU Sun Alkawarta Zurfafa Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare Karkashin Tsarin FOCAC
- Gwamnan Kaduna Zai Tallafa Wa Masu Zanga-Zangar #EndBadGovernance Da Aiki
Ministan kula da tsaftar muhalli Balarabe Lawal ya bayyana haka a Abuja a jawabinsa a yayin kaddamar da yin hadaka a tsakanin ma’aikatarsa da kuma shirin hadaka na kasa yaki da bolar robobi a kasa wato NNPAP.
Balarabe wanda kuma shi ne, shugaban shirin ya bayyana cewa, taron na da matukar mahimmanci wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.
Lawal ya bayyana cewa, Nijeriya ta zamo a kan gaba wajen samun yawan bolar robobin da ke zuwar ako ina a kasar, wanda hakan ke ci gaba da zamowa babban kalubale ga kasar.
A cewar ministan, ta hanyar kwashe wadannan bolar robobin, za a iya samar da ayyukan yi da habaka kananan da manyan sana’oin hannun, wanda hakan, zai janyo ra’ayin masu son zuba jari daga ketare na kai tsaye.
Ministan ya kara da cewa, a watan Fabirairun 2021 ne, Nijeriya ta yi hadaka da kungiyar yakar zubar da bolar robibin ta duniay wato GPAP bisa nufin kokarin da kasar ke kan yi a yakar gurbarbata muhalli.
Ya ci gaba da cewa, a watan Mayun 2023, ma’aikatarsa da hadaka da GPAP, inda aka kadamar da aikin yakar zubar da bolar robobin a cikin kasar.
Ita kuwa a na ta jawabin, Daraktar ta GPAP Madam Clemence Schmid, ta ce, kaddamarwar ta yau, ta nuna cewa, ba wai kawai maganar kaddamawa ake magana ba.
Ta ce, kungiyar ta mayar da hankali ne wajen ganin yadda za ta bayar da gudunmawarta wajen ganin ana ci gaba da tsaftace kasar.
Madam Clemence ta kara da cewa, tun a 2021, Nijeriya da kungiyar ta GNPAP sun kasance a kan gaba wajen sarrafa bolar robobin domin s samar da kudaden shiga.
Darakatar ta bayyana cewa, muna yin murna da wannan hadakar duba da irin dimbin mahimancin da take da shi, musaman ga ma;aikatar ta muhallin da kuma kungiyar a gafe daya da ma;aikatar ke jagoranta da kuma jami’na mu.
Madam Clemence ya sanar da cewa, kungiyar a yanzu ta na kan aiki a kasashe 175.