Wani abu ya fashe a kasuwar Terminus ada ke Jos, babban birnin Jihar Filato, da safiyar Talata, wanda ya jefa jama’a cikin tsananin fargaba.Â
Fashewar, wadda ta auku da misalin karfe 10:30 na safe, ta jikkata mutane da dama, sannan akwai yiwuwar rasa rayuka.
- IPMAN Da Matatar Dangote Sun Kulla Yarjejeniya Kan Dakon Mai Kai-Tsaye
- ‘Yan Bindiga 3 Da Mai Yin Safarar Makamai Sun Shiga Hannu A Taraba
Ko da yake ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani tukuna.
Shaidu sun bayyana yadda jama’a sun shiga rudani bayan fashewar abun.
“Na ji karar fashewar wani abu mai karfi kuma sai na ga mutane suna gudu suna ihu cike da tsoro,” in ji Gyang Buba, wani mai sayar da kaya a kasuwar.
Jami’an aikin ceto, ciki har da ‘yansanda da asibitoci, sun isa wajen da gaggawa, inda suka rufe yankin yayin da ake fara bincike.
Rundunar ‘Yansandan Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa ba tukuna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp