An sanya hannu kan yarjejeniyar karbuwa ta amfani da jiragen sama kirar kasar Sin samfurin C929 na daukar fasinjoji, da kamfanin sufurin jiragen sama na Air China. Jirgin samfurin C929 shi ne irin sa na farko mai cin dogon zango, da fadin daukar fasinjoji masu yawa, wanda aka kera bisa mizanin ingancin sufurin sama na kasa da kasa.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a Talatar nan, tsakanin kamfanin COMAC da kamfanin Air China, a yayin taro karo na 15, na baje kolin harkokin sufurin sama na kasa da kasa na Sin, da sauran nune-nunen jiragen sama, lamarin da ya sanya kamfanin Air China zama na farko da ya amince ya yi amfani da jirgin a harkokin sufurinsa.
Matsakaicin samfurin jirgin na C929 na daukar fasinjoji 280, yana kuma tafiyar da ta kai kilomita 12,000, wanda ya sanya shi zama jirgi da ya cika ka’idojin bukatun sufurin sama na kasa da kasa da na yankuna. (Mai fassara: Saminu Alhassan)