Kudirin zartaswa da ke gaban majalisun tarayya guda biyu na dokar sake fasalin haraji ya raba kan ‘yan majalisa daga yankin arewacin kasar nan.
Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Ali Ndume a wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan ya goyi bayan gwamnonin arewa da kungiyar tuntuba ta arewa (ACF), wadanda a tarurruka daban-daban suka yi watsi da kudirin dokar.
- Katsewar Lantarki: Masu Masana’antu Sun Kashe Naira Biliyan 238.3 Wajen Samun Wuta
- Bankin Duniya Da Hukumar Lamuni Ke Yi Wa Tsarin Ilimin Nijeriya Zagon-kasa – ASUU
Ndume a cikin sanarwar ya yi nuni da cewa, manufofin tattalin arziki na gwamnati mai ci sun talautar da al’umma, sannan kuma ya yi ikirarin cewa sake fasalin harajin zai kara wa talakawan Nijeriya matsin tattalin arziki.
Ya ce, “Wannan harajin da suke magana a kai, mun kusan rasa masu matsakaicin karfi a Nijeriya. Ko kana da shi ko ba ka da shi. Wadanda suke a tsakiya ana matse su. Idan ’yan Nijeriya za su iya biyan wadannan haraji, ba komai.
“Amma a halin da ake ciki yanzu, kara haraji ba mafita ba. Ba zan goyi bayan wani karin haraji ba.”
Sai dai da yake magana a ranar Litinin a Abuja, dan rajin kare hakkin Bil’adama kuma tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta 8, Shehu Sani, ya yi ikirarin cewa Sanata Ndume da wasu da ke kalubalantar shirin garambawul na harajin da ake shirin yi ba magana ce ta ilimi ba.
Ya ci gaba da cewa arewa kamar sauran sassan kasar nan za su ci gajiyar wannan sauyi na haraji.
Ya dage kan cewa kudirorin sake fasalin harajin ba su shafi arewa ba kamar yadda Ndume da makarrabansa ke bayyanawa, amma arewa ta tsaya kyam wajen yin kwaskwarimar da za ta sanya harajin VAT a hannun kowace jiha don sarrafa shi.
Sani ya ce wannan garambawul na iya haifar da sauyi daga tsarin haraji na baya da kuma sabon tsarin samar da kudaden shiga, domin zai magance matsalolin ‘yan kasuwa da za su iya yin duk wani abu don kaucewa kudaden haraji da kuma neman hana harajin da ba dole ba.
Ya yi gargadin cewa tattalin arzikin kasar zai yi matukar kaduwa idan aka soke kudirorin gyara haraji, inda ya yi Allah-wadai da kin amincewar da gwamnonin jihohin arewa suka yi na sake fasalin. Ya shawarci gwamnonin jihohin da su sa masu ba da shawara su yi nazari a kan kudirin, idan ba su da lokacin yin shi da kansu.