Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga Babban Taron Harshen Sinanci na Duniya na Shekarar 2024 wanda aka bude a birnin Beijing, yau Juma’a.
A wasikar tasa, Shugaba Xi ya taya kwalejin Confucius murna bisa cikarsa shekaru 20 da kafuwa.
- Mizanin Hajoji Da Hidimomi Da Masana’antun Kasar Sin Ke Samarwa Ya Karu Da Kaso 5.3 Bisa Dari A Watan Oktoba
- An Yi Garkuwa Da Sama Da ‘Yan Nijeriya 971 A Watan Oktoban 2024 – Rahoto
Xi ya ce, harshen Sinanci, wanda ke kunshe da hikimomin wayewar kan Sinawa da aka dade da su shekaru aru-aru, wani muhimmin samfurin al’adun al’umma ne da kasar Sin ta samarwa duniya.
Xi ya ce, nauyin da ke wuyan kasar Sin, a matsayinta na kasa mai amfani da harshen gado, shi ne bayar da tallafi, da saukaka wa al’ummomin duniya wajen koyo da koyar da ilimin Sinanci.
Xi ya bayyana fatan cewa taron zai kara sada zumunci, da cudanya, da cimma matsaya, da kuma gina gadojin hada alakar harsuna, da fahimta da amicewa da juna, da kuma koyo daga wayewar kai daban-daban, ta yadda hakan zai ba da gudunmawa ga gina al’umma mai makomar bai-daya saboda dan Adam. (Abdulrazaq Yahuza)