Masu ruwa da tsaki a harkar kiwon dabbobi, sun bayyana matukar jin dadi da kuma alfaharinsu ga Cibiyar Binciken Dabbobi ta Kasa (NAPRI) da ke Zariya a Jihar Kaduna.
Sun sanar da hakan ne, a wajen taronsu na masu ruwa da tsaki da suka gudanar a Jihar Kaduna.
- Yadda Gwamna Nasir Idris Ya Daura Damarar Bunkasa Ilimi A Jihar Kebbi
- Shugaba Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Babban Taron Harshen Sinanci Na Duniya
Masu ruwan da tsakin, sun fito ne daga yankin Arewa maso yamma; domin gudanar taron bita na kwana daya; wanda ya gudana a jihar ta Kaduna.
Akasarin makiyayan a jawabansu daban-daban a wajen taron, sun bayyana cewa; sun samu ilimin fadakarwa daga wannan cibiya, musamman a kan amfani da dabarun zamani na kiwon dabbobi.
Kazalika sun bayyana cewa, ilimin da suka samu daga cibiyar; ya kara bunkasa sana’ar tasu ta kiwon dabbobi, wanda kuma hakan ya kara habaka tattalin arzikinsu baki-daya.
Ita kuwa, Daraktar Cibiyar Farfesa Clarance A. Mawo Lakpini; a jawabinta a wajen taron ta bayyana cewa, cibiyar a shirye take domin bayar da gudunmawarta na kara ilimantar da masu sana’ar kiwo, musamman a Arewacin Nijeriya kan yadda za su rungumi dabarun kiwon dabbobi na zamani.
Ya ce, babu wata cibiyar bincike da ta tsaya a kan manufarta tamkar wannan cibiyar ta NAPRI.
Ya bayyana cewa, cibiyar na bukatar kula ta musamman bisa la’akari da nau’in dabbobin da take kulawa da su a duk rana.