A yayin da Nijeriya ke ci gaba da fusknatar kalubalen tattalin arziki da kuma hauhawar farashin kaya, wanda aka ruwaito cewa; shi ne mafi kamari a cikin shekaru 17 da suka wuce, hakan ya kuma shafi masu sana’ar kiwon kajin gidan gona, inda wasu masu sana’ar a Jihar Kano; tsadar ‘yan tsakin da abincinsu ta tilasata su dakatar da sana’ar.
Wani daga cikin masu sana’ar a jihar, Bala Idris ya sanar da cewa; tuni wasu daga cikinsu suka durkushe, sakamakon wannan matsala; inda wasu kuma da dama ke ci gaba da fafutukar lalubo mafita dangane da wannan kalubale da fannin ke fuskanta a jihar.
- Rikicin PDP: A Daina Maganar Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2027, A Maida Hankali Kan Jam’iyya –Saraki
- Mutfwang Ya Amince Da Mafi Karancin Albashi Na N70,000 Ga Ma’aikatan Filato
Wasu masu sana’ar kuma su ma sun bayyana cewa, farashin abincin kaji da kuma na ‘yan tsakin; ya fi tashi a cikin watan Nuwamba zuwa watan Disamba, amma a cikin wannan shekarar; tashin farashin ya fi yin kamari matuka, sabanin shekarun baya.
Wasu masu ruwa da tsaki a fannin da ke a jihar, Yakubu Ibrahim; wanda ke da gonar kiwon kajin da ake kira ‘Albarka’ ya sanar da cewa, saboda kalubalen biyu a yanzu, baya iya gudanar da aikin kamar a baya, inda ya kara da cewa; a baya ba su taba fuskantar irin wannan kalubale ba.
Ibrahim ya ce, akwai abubuwa da dama da suka jawo hakan wadanda suka hada da tsadar kajin da abincinsu, inda hakan ya jawo wasu ke barin ko ficewa daga sana’ar.
Ya kara da cewa, ana kuma fuskantar kalubalen masu yin kyankyasar ‘yan tsaki a jihar, inda ya kara da cewa; daukacin ‘yan tsakin ana shigo da su ne daga kudancin kasar nan, domin akasari ba a cika samun kamfanonin da ke yin kyankyasar ‘yan tsakin a jihar ba.
Ibrahim ya kara da cewa, masu kiwon kajin da ake kira da ‘Broilers’ a turance a jihar, su ne suka fi fuskantar wannan kalubale; domin farashinsu ya tashi matuka, wanda kuma ba a taba ganin hakan a baya ba.
A cewarsa, akasarin hakan ya fi afkuwa a lokacin bukukuwan karshen shekara da kuma lokacin gudanar da bikin Kirismeti, domin masu kiwon suna ci gaba da kiwon nasu ne har tsawon wata uku ko hudu kafin ‘yan tsakin su girma.
“Masu kiwon kaji da ake kira ‘Broilers’ a turance a jihar, su ne suka fi fuskantar wannan kalubale; domin farashinsu ya tashi matuka wanda kuma ba a taba ganin hakan a baya ba”.
Bincike ya nuna cewa, a yanzu haka ana kara samun bukatar kajin, inda hakan kuma ya shafi rabar da kajin a yankunan Arewa.
A yanzu dai, ana sayar da ‘yan tsakin kyankyasar kwana daya a kan Naira 800, inda kuma ba a iya sayen ‘yan tsakin da aka kyankyashe a cikin sati biyu ganin cewa kowane daya ana sayarwa a kan Naira 1,000; kuma babu wanda zai yarda ya sayi kowane daya a kan Naira 2,000.
Shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin, Mansur Shehu Kiru; mai gonar kiwon kajin da ake kira da ‘Rahama Agro’ ya bayyana cewa, ya rage yawan kajin daga 2,000 zuwa 400, sakamakon tsadar safararsu daga garin Ibadan zuwa Kano.
Ya ci gaba da cewa, magungunan kajin ma sun yi tashin gwauron zabi, inda ya kara da cewa; wannan ma babban kalubale ne da masu sana’ar ke fusktanta a jihar.
Ya ce, a ‘yan tsakin na ‘broiler’ a shekarar da ta wuce, ana sayar da duk guda daya a kan Naira 500; amma yanzu farashin ya kai daga Naira 800 zuwa Naira 850.
Mansur Shehu, a baya ana sayar da buhun abincin ‘yan tsakin a kan Naira 3,500, amma yanzu farshin ya kai daga Naira 8,000 zuwa Naira 9,000.
Shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin, Zaharaddin Yakasai; wanda ke da gonar kiwon da ake kira da ‘Yaks’ a Jihar Kano ya sanar da cewa, abincin kajin ya yi matukar tsada a bana, musamman saboda matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta.
Zaharaddin Yakasai ya bayyana cewa, saboda wadannan kalubale wasu masu sana’r suka dakatar da ita, domin tafiyar da fannin a halin yanzu; akwai matukar wahala.
Ya sanar da cewa, idan ka lissafa za ka ga ba wata ribar kirki muke samu ba, inda ya ce; wasu na barin sana’ar wasu kuma sun rage yawan adadin wadanda suke kiwatawa.
A cewar Zaharaddin Yakasai, muna matukar bukatar gwamnati ta kawo mana dauki, musamman ganin yadda fannin ke taimakawa wajen samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma wadanda ba na kai tsaye ba a jihar, musamman a tsakanin matasan jihar.
Zaharaddin Yakasai, ya kuma koka a kan yadda duk da wadannan kalubale da masu sana’ar ke ci gaba da fuskanta, amma masu karbar haraji tun daga kananan hukomomi har zuwa matakin jiha; ba sa daga musu kafa, inda ya sanar da cewa; masu karbar harajin na karbar daga Naira 100,000 zuwa Naira 300,000.
“Akwai matukar bukatar gwamnati ta kawo mana dauki, musamman ganin yadda fannin ke taimakawa wajen samar da ayyukan yi kai tsaye da kuma wadanda ba na kai tsaye ba a jihar, musamman a tsakanin matasa”.
Shi ma, wani dilan ‘yan tsaki da sauran tsintsaye a jihar; Abdurrahman Suleiman Tarauni ya bayyana cewa, sana’ar a halin yanzu ba ta tafiya yadda ya kamata, inda ya kara da cewa; a yanzu ana sayar da abincin kajin daga Naira 8,000 zuwa Naira 9,000, inda hakan ya sa mutane ba sa iya saya.