Kasar Peru makwafciyar kasar Sin ce ta bangaren tekun Pacifik, kuma fadadar kusancin sassan biyu ta fuskar tattalin arziki, da hadin gwiwar cinikayya, da musayar al’adu, na ci gaba da matso da kasashen biyu kusa da juna, a matsayin kawaye kuma makwafta a yankin tekun Pacifik.
Yayin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping kasar Peru, a karon farko, kafar watsa labarai ta CGTN, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani, da cibiyar zurfafa bincike game da harkokin kasa ta Peru, sun kaddamar da wani binciken jin ra’ayin jama’a, game da karbuwar kasar Sin tsakanin al’ummun kasar Peru a shekarar 2024 inda ’yan kasar Peru 1,111 suka bayyana ra’ayoyinsu.
- Sin Ta Harba Kumbon Tianzhou-8 Na Dakon Kayayyaki Zuwa Tashar Binciken Samaniya Ta Tiangong
- Bankin Duniya Da Hukumar Lamuni Ke Yi Wa Tsarin Ilimin Nijeriya Zagon-kasa – ASUU
Sakamakon binciken ya nuna yadda masu bayyana ra’ayoyin suka yi amanna da kawancen gargajiya tsakanin Sin da Peru, da nasarar hadin gwiwarsu, tare da fatan ganin an gina “Salon kasar Peru” na inganta alakar Sin da kasashen Latin Amurka, da bunkasa hadin gwiwa bisa matsayin koli, tsakanin kasashe masu tasowa da masu saurin samun ci gaba.
A matsayin Sin na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, nasarorin da ta cimma, da mahangarta ta zamanantarwa, sun samar da wata gogewa, da tarin damammaki ga kasashe masu tasowa da masu saurin samun ci gaba.
Kazalika, sakamakon binciken ya nuna yadda masu bayyana ra’ayoyin suka gamsu da nasarorin da kasar Sin ta samu, ta fuskar ci gaba mai inganci da bude kofa bisa matsayin koli.
Cikin masu bayyana ra’ayoyin, kaso 97.2% sun yaba da saurin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. Kana kaso 94.8% sun amince cewa tattalin arzikin kasar zai ci gaba da bunkasa. Har ila yau, kaso 89.9% sun gamsu da muhimmancin gudummawar kasar Sin ta fuskar ingiza daidaito a tsarin rarraba hajojin masana’antu tsakanin sassan duniya.
A daya hannun kuma, kaso 85.7% na ganin Sin na da babbar kasuwa wadda ke bude, kuma mai karbar takara ta adalci. Akwai kuma kaso 96.6% da suka yabawa kasar Sin, bisa muhimmiyar gudummawa da ta bayar wajen farfado da tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)