A ranar Litinin da ta gabata ce, gwamnatin Jihar Bauchi ta tashi tsaye domin ganin ta tunkari matsalar yunwa da karancin abinci, inda ta kafa kwamitin saye da adana kayayyakin abinci domin fito da su a lokacin da suka fara wahalar samuwa domin shigar da su cikin jama’a.
Kwamitin wanda zai shiga lungu da sako na jihar wajen sayen kayan abinci daga hannun manoma a lokacin girbi domin yin goyayya da masu zuwa su saya daga jihar zuwa wasu jihohi da ma wasu kasashe.
- Mata A Dage Da Karatu Yin Haka Taimakon Kanku Ne Da ‘Ya’yanku – Zainab Ahmad
- Shaharrun Mutanen Da Suka Halarci Bikin Auren ‘Yar Kwankwaso
A cewar gwamnan jihar, Bala Muhammad a yayin rantsar da mambobin kwamitin, an yi wannan tsarin ne domin yaki da yunwa da fatara da kuma taimaka wa talakawan da suke jihar, uwa-uba da kuma daukan matakan shawo kan matsin rayuwa da ake fuskanta.
Ya ce, abun kunya ne kamar Jihar Bauchi da Allah ya huwace mata manoma da albarkatun noma a wayi gari a ce ana bukatar abinci, ya ce, sun nazarci cewa babbar matsalar kawai shi ne manoma na sayar da kayan abincin ga wasu da suke zuwa daga waje domin saye da fitar da su, don haka ba za su zura ido suna bari hakan na faruwa ba.
Sai dai, ya ce, ba za su hana manoma sayar da kayan amfaninsu ga kowa ba, illa za su yi hikima da dabarar yin gasa wajen saye domin taimaka wa al’umman jihar a lokacin da za a shiga neman abinci gadan-gadan.
Gwamnan ya sanar da ware naira biliyan uku ga kwamitin a matsayin kudin jari, ya kuma sanar da cewa, akwai damar za a iya kara wa kwamitin kudade domin ba su damar zuwa ko’ina su sayo kayan abinci a wajen manoma domin ajiyesu har zuwa lokacin da za a fito da su wajen taimaka wa jama’a.
Bala ya hori kwamitin za su yi amfani da hikima da dabarbarunsu domin kyautata tattalin arziki da kuma taimaka wa jama’a wajen rage yunwa da fatara.