Fitaccen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke (Davido), ya sanar da shirin ba da tallafin Naira miliyan 300 ga marayu a fadin Najeriya ta hannun gidauniyarsa ta Davido Adeleke Foundation (DAF).
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin, inda ya ce,
“Kamar yadda na saba a ranar haihuwata, bana maimakon biki, za mu ba da tallafi ga marayu da wata kungiya da ke yaki da matsalar shaye-shaye. Wannan shekarar za ta kasance N300m.”
Davido ya kafa DAF a shekarar 2022 domin tallafa wa yara marasa galihu a Nijeriya, inda ya haɗa kai da wasu ƙungiyoyin agaji don cimma wannan buri. A watan Yuli 2023, Davido ya sanar da cewa DAF ta raba sama da Naira miliyan 200 ga marayu, wanda ya inganta rayuwar yara 13,818. Ya kuma yi alkawarin ci gaba da irin wannan tallafi a shekarar 2024.
Tarihin aikin jin ƙansa dai ya fara ne a shekarar 2021 bayan murnar ranar haihuwarsa, lokacin da ya tara Naira miliyan 200 ta hanyar raba lambar asusun ajiyarsa a Twitter. Nan take ya rabar da duk adadin da ya tara, tare da ƙarin Naira miliyan 50 daga aljihunsa, ya bayar ga marayu da kuma ƙungiyar Paroche Foundation wacce ke yaƙi da shaye-shaye.
Davido ya ce,
“Na kafa wannan gidauniya ne domin tallafa wa mutane masu buƙata tare da tabbatar da cewa ayyukan jin ƙai suna gudana yadda ya kamata. Kawo yanzu mun tallafa wa gidajen marayu da dama, wanda hakan ya inganta rayuwar dubban yara.”