Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyan 95 ne za su yi zabe a 2023.
Ta kara da cewa ba dukkan wadanda suka yi rajisitan katin zaben da aka kammala a wannan makon za su samu damar jefa kuri’a.
- NIS Ta Sauya Wuraren Aiki Ga Manyan Jami’ai 69
- Gwamnatin Gombe Ta Kafa Kwamitin Sayarwa Da Raba Takin Zamani Don Saukaka Wa Manoma
Kwamishinan yada labarai na hukumar INEC, Mista Festus Okoye shi ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin gudanar da wani shiri a gidan talabijin na Arise Tb.
Okoye ya bayyana adadin yawan wadanda za su jefa kuri’a a zaben 2023, wanda adadinsu ya kai miliyan 95.
A cewarsa, akwai yuwuwar hukumar za ta cire da yawan wadanda suka yi rajistar daga kididdigar hukumar tare da hana su katin zabe saboda sun yi rajista fiye da guda daya.
Okoye ya tunatar da cewa na farko da na biyu na aikin yin rajistan, an cire fiye da kashi 46 na wadanda suka yi rajista daga kididdigar hukumar sakamakon yin rajistan fiye da guda daya.
Ya ce, “Abun takaice ne a ce an kammala yin katin zabe a yanzu, amma saboda za mu hada dukkan kididdigan wadanda suka amshi katin zabe da muka kammala a kwanan nan tare da amfani da na’urarmu mu cire wadanda suka yi rajista fiye da guda daya.
“Kamar yadda muka sanar, lokacin da muka kammala goje adadin wadanda suka ka yi rajista fiye da guda daya na farko da na biyun aikin rajistar, mun cire sama da kashi 46 wadanda suka yi rajista fiye da guda daya.
Domin haka, za mu yi haka a aikinmu na uku da na hudu domin goje wadanda suka yi rajista fiye da daya.
“Bayan haka, za mu yi hakan a dukkan bayananimu, saboda sashin na 19 (1) na dokar zabe na 2022, ta tilasta wa hukumar zabe ta bayyana wadanda suka yi rajistar zabe a dukkan wuraren yin katin zabe da ke kananan hukumomin Nijeriya guda 8,809.
“Muna tsammanin za a samu wadanda suka yi rajistar zabe guda miliyan 95, inda za mu lika hotunan sama da miliyan 20 a shafi guda dubu biyar a wadannan wuraren rajista, daga baya sai mu lika sauran da suka rage.”
Kwamishinan INEC ya kara da cewa ba dole ba ne a sake kara wa’adin yin rajistan zabe, saboda idan har aka kara, to zai shafi sauran wasu ayyukan na shirye-shiryen zaben 2023.
Ya ce, “Mun bayar da isasshen lokaci ga wadanda suka cancanci yin rajistan zabe, wanda muka bayar da tazarar yin rajistar har na tsawon watanni 13.
“Lokacin da muka kara wa’adin wata daya na yin rajistar zabe, sai da muka kara yin hayan ma’aikata a dukkan wuraren yin katin zabe, sannan mun kara wasu na’urori a dukkan cibiyoyin yin rajista da suka gudana.
Haka kuma mun kara lokacin yin katin zaben tun daga karfe tara har zuwa karfe biyar na yamma, ciki har da ranakun Asabar da Lahadi.
Amma abun takaicin shi ne, mun kammala wannan aiki a ce sai mun kara wani wa’adi, aikinmu na zabe muna tafiyartar da shi ne kamar yadda doka ta tanada. Idan muka kara wani wa’adin yin rajista, to zai shafi jaddawalin ayyukan zaben 2023.”
Kwamishinan ya cewa sun bai wa jama’a duk irin lokacin da suke bukata don mallakar katin zabe. A kan haka ya ce ba za su sake tsawaita lokacin yankar rajistar ba, lura da yadda lokaci ke kara kure musu.
INEC ta ce tana so ta mayar da hankali ne ga sauran ayyukan da ke kan jadawalin zaben na 2023, kuma dole sai ta rufe yankar katin ne za ta iya samun ci gaba.
A ranar 28 ga watan Yuni ne, hukumar zaben ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar zuwa ranar 31 ga watan Yulin 2022, bayan bukatar hakan daga bangarori daban-daban na kasar.