Duk yadda shari’un zabe suka kaya musamman na gwamna, a Kotunan daukaka kara koko Kotun Koli, kuskure ne babba tare da kidahumanci raunana talakawa su yarda a yi amfani da su, wajen tayar da tarzoma a cikin kowane bangare na wannan Kasa. A hankalce, yayinda jam’iyyarka ta sha kasa a kotun daukaka kara, sai ku garzaya ne zuwa ga kotun koli, kamar yadda aka tsara shimfide cikin Kundin Tsarin Mulki na Kasa, 1999.
Ga mai bibiyar irin yadda lamarin shari’un da ke da jibi da siyasa ke gudana a wannan Kasa a jiya da yau, sai a ga hatta wanda yake bisa kujerar shugaban Kasa, hukunce-hukuncen kan zo masa ba irin yadda yake da muradi ba. Ta faru a lokacin da Atiku Abubakar ke bisa kujerar mataimakin shugaban Kasa, ya sha rangala shugaban Kasa na lokacin da kasa, a kotunan wannan Kasa, kuma ala-tilas haka shugaban Kasar ke amsar hukuncin da ba haka yake son gani ba, ina ga talaka irina irinka kuma?.
- Xi Jinping Ya Halarci Zaman Rufe Taron Kolin G20 A Rio De Janeiro
- Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Tashar Mota Ta Zamani A Gusau
Yaudarar kai ne, talakan Najeriya ya yi kokarin ta da husuma, kawai don an kwace kujerar wani dan siyasa da yake goyon baya musamman gwamna, duba da irin abubuwan takaicin da ke biyo baya ga irin wadancan talakawa da ke tarar aradu da ka. Duk talakawan da ke tayar da wata husuma a wannan Kasa, da sunan wani dan siyasa, a duk sa’adda lamura suka cabe, sai a ga cewa, su da iyalansu ne da ‘ya’yansu da kuma iyayensu ne ke kwana ciki, tare da girbar nadama.
Tun daga Shekarun 1950s zuwa yau, ake ta asarar dubban rayukan jama’a cikin wannan Kasa da sunan siyasa. Asarar rayukan, kan faru ne ta mabanbantan sabubba. Wasu rayukan talakawan da ake rasa su a wancan lokaci (1950s), na faruwa ne, a kan hanyarsu ta fafutukar samun cikakken ‘yanci irin na siyasa, daga farare da kuma bakaken Turawa. Tun da a lokacin, za a samu cewa, Turawan mulkin mallaka ne suka mara baya ga wasu jagororin jam’iyyar siyasar da ke binsu sau da kafa sabanin wasu jam’iyyun. Da yawan mutane a wancan lokaci, an daure su, an ci tararsu, an kwace dukiyoyinsu, an kore su ko sun gudu daga mahaifarsu, uwa uba, da damansu an kashe su ne. An make wasunsu da sanda ko gariyo, akwai wadanda ma aka yi wa yankan rago a bainar jama’a. Irin wannan ta’ada, ta rasa rayukan talakawa a wancan lokaci, ta fi yawaita ne a arewacin wannan Kasa. Na’am, a kudancin Kasar ma, musamman kudu maso gabas, wasu matasa, sun hadu da fushin masu jajayen kunnuwa (Turawa), inda da damansu suka bakunci lahira sakamakon tutsunsu ga masu mulki, na a ba su cikakken ‘yanci na irin siyasar da suke da muradin ta wanzu a lardinsu.
Duk da banbancin tunani ko fassara da ake alakantawa ga mace-macen da suka faru da sunan siyasa a Shekarun 1950s, sai a ga cewa sama da kashi 98% na wadanda a ka kashe a wancan lokaci, ba su da wani gata da suka bari a Duniya, wanda zai ci gaba da tallafar dawainiyar iyalansu. Da ma su ke yin tiri-tiri da jigilar iyalan nasu, wajen ciyarwa da shayarwa tare da tufasarwa. Duk da cewa, a wancan lokaci abinci bai zamto wani kayan gabas irin wannan lokaci da muke ciki ba. ‘ya’yan masu mulki da sarakuna hada da na attajirai, a duk sa’adda aka gaiyaci mutane zuwa ga kyalayar da jinanensu da sunan siyasa, irin wadancan ‘ya’yaye ‘yan-lele na gida ne kwance cikin na’urar sanyaya daki, wasunsu ma na can Kasashen ketare ne tare da shan-gallarsu abinsu. Idan aka karkashe kunzumin tawagar talakawan, wadancan yara ‘yan-lele, sune fa kan gaba wajen morar gwamnatin.
‘ya’yan masu mulki nawa ne ake zargin, su, da iyayensu sun mayar da baitul malin al’umma da tamkar kayansu na gado?. Bugu da kari, a duk sa’adda talakawa suka ba da jininsu fi-sabili siyasa, a karshen lamari, mummunan zargi ne ke biyo baya. Ko mai karatu na iya tuna murnar da talakawa suka rika yi cikin wannan Kasa a Shekarar 2015, da sunan Baba Buhari ya ci zabe?. Abin tambayar shi ne, ta tabbata sama da mutum 100 ne suka mace sakamakon waccan murna ta ba gaira balle dan dalili, amma a karshen lamari, sukarsu Baba Buhari ya buge yi. Yana nuna muguwar wautarsu game da irin wancan bikin nuna murna da suka yi, wanda ya kawo rasa dimbin rayuka da dukiyoyi a wannan Kasa, musamman arewacinta.
Wane shiri gwamnatin Buhari ta yi, na agazawa iyalan wadancan masoya nasa da suka mace a kan titinan wannan Kasa, kawai saboda murnar ya lashe zabe? Cikinsu, wasu, su ke daukar nauyin duka hidimar iyalansu, da ma hidimar iyayensu. An wayigari sun mace a dalilin siyasa, babu wani shiri daga gwamnati na tallafar iyalansu ko iyayensu! Ba ma batun bai wa ahalinsu wani tallafi ba, bakar magana ce ma ta fito daga bakin wanda a sanadiyyarsa ne suka yi irin waccan mutuwa ta kunar bakin wake! Amma da mutum zai yi duba zuwa ga iyalan wancan shugaban Kasar da ake mutuwa dominsa, sai ya samu cewa duniya ce ta dawo musu sabuwa ful ko lamba. Cikin wadancan talakawa da suka mace a siyasar Baba Buhari, ba ma dan gwamna ba, a duk fadin Najeriya, a kawo mana wani dan kwamishina da ya yi irin waccan mutuwa ta fargar-jaji.
Hatta wadanda suka shiga bangar siyasa a Shekarun 1980s, ai za a samu cewa ‘ya’ya ne irin na Malam Shehu. Wani abin da mutum zai yi tsai tare da nazarta shi ne, a duk Shekara a nan Kano, a na gabatar da bukukuwan tunawa da Malam Aminu Kano, Alh. Abubakar Rimi da sauransu. Sai yaushe ne za a fara yin bikin tunawa da mutane irinsu su Sabo Wakilin Tauri, da Hadi na Fagge, da Tanko Mai Arna, da Saleh Maye?. Duka wadannan mutane da aka lasafto, sun yi gwagwarmaya a fagen siyasa tare da ba da jininsu wajen kare muradan jagororinsu na siyasa, to amma an wayigari, kwata-kwata ma ba a wani tunawa da su, daukacinsu a yau, suna can kwance cikin kabari.
A matakin Kasa ma haka ake bikin tunawa da manyan mutane irinsu Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Chief Nnamdi Azikwe, amma ba a yin bikin tunawa da wasu manya manyan ‘yan bangarsu da suke ba da jininsu don kare irin wadannan manyan mutane ‘yan kishin Kasa. Yaushe rabon da a yi bikin tunawa da ‘yan kungiyar “Zikist Mobement” a lardin Inyamurai? An manta ne da irin dauki ba dadin da suka rika yi da Turawan Mulkin Mallaka, da sunan siyasa? Mutum nawa cikinsu Turawan suka kashe?. Ashe ma gara shugabannin shi’a cikin wannan Kasa da suke yin bikin tunawa da irin mutanensu da aka kashe! Kuma za ka yi mamakin irin yadda suke tallafar iyalan wadanda suka mutum, karkashin wata Gidauniya da suka kira ta da “Mu’assasatul Shuhadah”.
Idan ya zamana cewa, an sha kashe mu da sunan kare manyanmu na siyasa cikin wannan Kasa, sannan, bayan kisan, babu wanda zai tallafi iyalanmu, babu ruwan kowa da maslahar iyalan namu, to menene fa’idar bayar da rayukan namu?. Gaskiyar magana ma ita ce, har gara irin wadanda suka ba da rayukan nasu a can Shekarun baya da sunan siyasa, domin kuwa, akasarin jagororin siyasun na wancan lokaci da gaske ne suke. Abinda ke kunshe cikin zuciyarsu, shi ne suke gudanarwa a aikace cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Kana ina, marigayi Malam Aminu Kano, duk da shi ya tsayar da gwamnoni biyu, Kano da Kaduna, aka zabe su dominsa, amma har ya bar Duniya gidansa babu injin wuta! Idan an dauke wutar lantarki, yadda talaka zai kwana cikin duhu, shi ma haka Malam zai kwana a duhu! Haka jagororin siyasar yau suke? Babbar toshewar kwakwalwa ce talakan yau, ya ba da jininsa saboda dan siyasar yau!!!.
Da arewacin Najeriya, da kudu maso yammacin Kasar, hada da kudu maso kudu ko kudu maso gabashin Kasar, a ina ne ake yin zaben gwamna da na shugaban Kasa duka lafiya ba tare da talakawa sun kashe kansu da kansu ba? A da, a kan yi kashe-kashen ne a lokutan zabukan cikin gida na jam’iyyu, da lokutan yawon kamfen, sannan da ranakun gudanar da zabuka. Ga dukkan alamu, irin wadancan wurare da talakawa ke kyalayar da jinanansu bai ishe su ba, yanzu kuma da dama cikin jagororin siyasa a arewaci da kudancin wannan Kasa, na son, su ingiza magoya baya ne zuwa ga ta da tarzoma bayan yanke hukuncin shari’un zabe musamman na gwamna.
Duk wasu kashe-kashe da ake yi a wannan Kasa da sunan siyasa, yaushe ne jama’ar Kasa ke ganin an hukunta wadanda ke yin kisan, koko wadanda ke daukar nauyin kisan?. Ai da zarar an dare bisa kujerar mulki, wanda ya yi kisan, da wanda aka kashe duka daya ne suke a wajen masu mulki. Hujja? Saboda duk wanda ya samu dafe madafun iko, ba zai kara waiwayar irin waccan tarzoma da aka yi ta kashe jama’a ba. Sau nawa ne za a ji an kaure da batun wani kisan kai da aka yi a lokutan zabe, amma da zarar an kammala zabukan, sai a ga kowa ma ya manta da batun kisan?. Mai mulki da sauran jama’ar gari, kowa zai manta da cewa, ka kashe ne, koko an kashe ka? Amma iyalanka da iyayenka fa?. Sune kadai wadanda za a bari da musifar rayuwa da takaici!!!.
A jam’iyyar APC a Kano, an zargi wani dan siyasa da ke cikin gwamnati, da kashe mutane a zaben da aka gudanar na wannan Shekara ta 2023. Bugu da kari, lokacin bude asibitin Hasiya Bayero, an zargi wani jigo a jam’iyyar NNPP da ingiza wasu matasa, da suka yi wa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ihu. Sai dai an kame su. Da wadancan da aka kashe, da wadannan da aka kame, wake maganarsu yanzu, daga cikin mutanen gari ko kuma gwamnati? Shi wancan ma da ake zargin ya yi kisan kai da bindiga, babu jimawa bayan zabe, sai gashi ga gwamna wajen wani daurin aure suna cafkewa da sunan gaisuwa!. To kuwa da mutum zai je ya samu iyalansu da iyayensu, anya zai ga suma sun manta, sun koma shan gallarsu?. Sai yaushe ne talaka zai yi hankali a Najeriya?.
Wani abin takaici da Allah wadai, batun azabtar da talaka da masu mulki ke yi yanzu, ko ingiza shi ya kashe ‘yan’uwansa, duka wannan bai ishe su ba, a’a, yanzu kuma suna daukar talakan ne zuwa Kasashen Waje, a turmushe shi, a cire masa koda ko wani sashin jikinsa, don dasawa a jikin ‘ya’yayensu. Allah ne kadai ya san adadin hanyoyin da masu mulki ke amfani da su a yau, wajen wawantar da tunanin talakawan wannan Kasa. Hatta wancan mai mulkin da ya rungumi wani dan talaka zuwa Kasar Ingila don cire kodarsa, ya kware ainun wajen amfani da ‘yan daba tare da jikkata mutane don ya ci zabe. A wasu lokuta ma, a kofar gidansa ne ake zubarwa da mutane jini, wai da sunan ‘yan adawar siyasa ne su. Shi ma na can cikin ukuba a yau, tasa ta same shi!
Ba ya ga zubar da jinin talakawa da shugabanni ke ingiza faruwar hakan, sai batun samun takara, ko samun wasu mukamai manya masu tsoka a gwamnati suka koma ga nasabar surkuta, ko ‘yan’uwantaka, koko wanda ke da karfin jakar tsaba. Sai harkar ta fara komawa cin amana da wawantar da tunanin masu tunani. Babu shakka karara a zahiri, mulkin masu mulki a yau cikin wannan Kasa tamu, bai damu da maslahar talaka ko ta iyalansa ba. Babban amfaninsa shi ne, ya fito ya yi zabe, daga nan, sai a lankafe shi a gida, a yi ta yi masa ruwan harsashin talauci da firgici! Sai a ware masu ido da kwalli a ci gaba da warbar haramtattaccen romon dimukradiyyar da gumin wasu ne yai silar samuwarsa, sai a mayar da su ‘ya’yan bora. Irin wannan dalili ne ke sanyawa cikin wasu Kasashen Afurka da aka yi juyin mulkin Soja, sai a ga jama’ar gari sun fito suna ta faman murna bisa titunan Kasar.
Ba ma fata ko goyon bayan juyin mulkin Soja a wannan Kasa. Haka ma, ba ma goyon bayan a rika amfani da jahilcin Talaka, a na ingiza shi zuwa ga haddasa fitintunu ko aikata kashe-kashe, wai da sunan kare muradan siyasa, wanda tsirarun mutane ne ke amfanarsa!