A tarihin duniya, kowane zamani kan gabatar da mafita ga matsalolinsa. Kazalika, bil Adama a yanzu yana fuskantar sabbin matsaloli, kamar tasirin sauyin yanayi, karancin wadatar albarkatun kasa, bala’in yunwa da har yanzu ke shafar mutane sama da miliyan 700 a duniya, babban rashin daidaiton kudin shiga tsakanin daidaikun mutane da kasashe, kwararowar masu kaura da matsalolin siyasa da na tattalin arziki da muhalli ke haifarwa, ga batun manyan laifuka na kasa da kasa, da habakar son kai da kariyar cinikayya a tsakanin kasashe masu arziki da ke illa ga manyan bukatun kasashe masu tasowa, duka wadannan matsaloli ne da ke addabar wannan zamani wadanda ke haifar da talauci da yunwa, kuma a kan su ne aka gina ajandar taron kolin G20 na bana.
A jiya Talata ne dai aka rufe taron kolin G20 wanda ya gudana a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, taron da tashe-tashen hankula guda biyu masu muni, daya na Gabas ta Tsakiya da kuma na Ukraine suka karkatar da hankalin mahalarta daga muhimman batutuwan duniya kamar talauci da kawar da yunwa. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada matsayin kasar Sin wajen tabbatar da hadin kai don samar da duniya mai adalci da ci gaba tare yayin da shugabannin kasashen duniya na G20 suka yi alkawarin yin aiki tare a kan wadannan kalubalen da duniya ke fuskanta tare da amincewa da samar da mafitar dakatar da tashe-tashen hankula da ke kawo cikas ga zaman lafiyar duniya.
Shugaba Xi Jinping bai gaza sanar da matakai daban daban don bunkasa ci gaban duniya ba, inda ya jaddada goyon bayan da Beijing ke bayarwa ga ayyukan samar da ababen more rayuwa a duniya, da tsarin shawarar “Ziri daya da Hanya daya”, da shirin hadin gwiwar fasaha don tallafawa kasashe masu tasowa da shirin ci gaban duniya, da shirin samar da tsaro na duniya, da shirin wayewar kai na duniya, wadanda suka kasance gudummawar kasar Sin ga kasashen duniya don gina ayyukan da za su taimaka wajen shawo kan manyan kalubalen da bil Adama ke fuskanta. Mahalarta taron sun yi tsarabar ayyuka guda takwas da shugaba Xi ya gabatar don tallafawa ci gaban duniya. Yana mai cewa, “da taku daya ake fara tafiyar mil dubu,” kuma kasar Sin a shirye take ta dauki matakai tare da dukkan bangarori domin samar da duniya mai adalci ta hanyar samun ci gaba tare. (Mohammed Yahaya)