Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa dakarunta sun kashe wani fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda, Munzur Ya Audu, da wasu 114 tare da kama ‘yan ta’adda 238 a cikin mako guda.
Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya ce rundunar sojin ta kuma rasa sojoji takwas (biyar a yankin Arewa maso Gabas da uku a Kudu maso Gabas) tare da kubutar da mutane 138 da aka yi garkuwa da su duk a cikin mako guda.
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudurin Wa’adi Guda Na Tsawon Shekara 6 Ga Ofishin Shugaban Ƙasa
- Kasar Sin: Ya Kamata Nahiyar Turai Ta Girmama Manufar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
Ya ce rundunar soji ta kara kaimi wajen ci gaba da daukar kwararan matakai a kan ‘yan ta’adda domin kawar da burbushinsu baki daya. “A bisa haka, muna tattara bayanan sirri, muna farautar su da kuma kai musu samame a wuraren da aka tabbatar da cewa maboyarsu ce.
“An kashe wani fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda mai suna Munzur Ya Audu a yankin Arewa-maso-Gabas a wani samame.”
Janar Buba ya ce, sojojin sun kwato makamai iri-iri 145 da alburusai iri-iri 3,825.
Ya ce sojoji suna yin kokari sosai don wargaza duk wani shiri na ‘yan ta’adda tare da lalata duk wani yunkurinsu.