Biyo bayan rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta fitar a cikin want Ukotobar 2024, na samun hauhawan farashin kayan masarufi, hakan ya nuna cewa, alumomin da ke a jihohin Sokoto, Edo, da Borno, sun fi sayen kayan da tsada
Rahoton Hukumar ya bayyana cewa, hauhawan farashin kayan a kasar nan, ya karu zuwa kashi 33.88 daga kashi 32.70 a watan Satumbar 2024.
- Gwamnatin Bauchi Ta Kaddamar Da Kwamitin Adana Kayan Abinci
- Shari’un Zabe: A Kauce Wa Tarzoma Duk Yadda Ta Kaya
Hauhawan ta faru ne, akasari saboda tashin farashin man fetur, wanda daga shekara zuwa shekara, ya kai kashi 6.55, wanda a watan Okobar 2023 ya kasance kan kashi 27.33.
Alkaluman na NBS sun nuna cewa, yawan hauhawan na farashin da ta karu a watan Okubar 2024, ya kai kashi 39.16, idan aka kwatanta kashi 7.64 da aka samu a watan Okotobar 2023, wanda ya kai kashi 31.52.
Hukumar ta danganta hauwan farashin kayan abincin kamar na Masara, Dawa, Shikafa da sauransu.
Kazalika, a daga shekara zuwa shekara, karin farashin kan kayan abinci a jihar Sokoto ya kai kashi 52.18, inda a jihar Edo ya kai kashi 46.55.
Bugu da kari a jihar Borno da ya kai kashi 45.85, inda kuma a jihar Kwara, ya kai kashiu 31.68, jihar Kogi ya kai kashi 33.30, inda a jihar Ribas, ya kai kashi 33.87.
Har ila yau, daga wata zuwa wata hauhawan farashin a watan Okotubar 2024, ya karu da kashi 5.08 a jihar Adamawa, a jihar Sokoto ya karu da kashi 486.
A jihar Yobe ya karu da kashi 4.34, inda a jihar Kwara, ya karu da kashi 1.11, inda a jihar Ondo ya karu da kashi 1.3 a jihar Kogi kuma ya karu da kashi 1.50.
Wadannan alkaluman sun nuna cewa, hauhawar ta karu a watan Okotobar 2024, idan aka kwatanta da ta 2024.
Haka zalika, daga wata zuwa wata hauhawar a watan Okutobar 2024, ta karu da kashi 2.64 wanda ya karu zuwa kashi 0.12 a cikin watan Satumbar 2024 zuwa kashi 2.52.
Wannan ya nuna cewa, a watan Okobar 2024,an samu karin farashin kayan mai yawa a watan Satumbar 2024.
Daga shekara zuwa shekara a wata Okutobar 2024 hauhawan farashin kayan a cikin birini ta kai kashi 36.38, wanda ya haura kashi 29.29, a watan Okutobar 2023.
Bugu da kari, daga wata zuwa wata, a cikin birni a cikin watan Okutobar 2024, ya karu da kashi 2.75, wanda hakan ya nuna cewa, an samu karin da ya kai 0.08 idan aka kwatanta da karin da aka samu a watan Satumbar 2024, wanda ya kai kashi 2.67.
Idan aka kwatanta da hauhawar da aka samu a cikin birnia cikin shekara daya, ta kai kashi 34.52 a watan Okubobar 2024, wanda idan aka kwatanta da watan Okutobar 2023, ya kai kashi 24.76.