Shafin Taskira, shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne akan wannan sabuwar kungiyar da ta fito mai suna Lakurawa. Meye ra’ayinku akan wannan sabuwar kungiya?
Hassan Tijjani
Sojin Nijeriya sun ce Lakurawa na da alaka da kungiyar IS kuma suna aiki a jihohin Kebbi da Skkwato, kuma sun fito ne daga kasashen Mali da jamhuriyar Nijar inda suka kutsa Nijeriya. Lokaci na farko da Lakurawa suka bayyana a Nijeriya shi ne a shekarar 2018, a lokacin da suka fara taimakawa jama’a wurin yakar ‘yan bindiga kamar yadda rahotanni suka tabbatar. To sai dai daga bisani alaka ta yi tsami tsakanin Lakurawa da mutanen gari, bayan da jama’a suka zarge su da fara sace musu shanu da kuma kakaba musu dokoki.
Bilkisu Maharazu
Assalamu alaikum, Ra’ayina akan wannan sabuwar kungiya mai suna lakurawa ba abinda zance sai Allah ya kawo mana sauki ya kawo karshen wadannan fitintinun, domin wata majiya suna cewa wadannan kungiyoyi suma wani sa shene na Boko Haram , duk dai magana dayace da ‘yan” kidnapping domin basuda bambanci da su tunda duk ta’addanci suke ganin cewa gwamnati bata dauki wani mataki na masu garkuwa da mutaneba shi yasa suka bullo da wata kungiyar domin masu magana na cewa kowa ya samu dama sai yayi shanya domin da basu samu da maba da Basu shigo ba.
Bugu da kari, idan har ba dama suka samu ba me yasa basu shiga kuduba sai Arewa saboda anaso a bata Arewa shi yasa, Kuma a ka,ida ai ba,a shi ga kowace kasa kai tsaye batare da izini ba sai Najeriya da batada tsaro duk wanda yado za,abar shi ya shiga harda criminals saboda da zarar an bada kudi sai abude kofa a shiga batare da binciken su wayeba.
Usman Sani
Bayyanar wata sabuwar kungiyar ta’addanci mai suna Lakurawa a Kebbi abin damuwa ne, yana nuna bukatar karin tsaro da tattara bayanan sirri a Najeriya. Hakan kuma yana jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin gano irin wadannan barazanar da wuri da kuma magance su. Gwamnati da hukumomin tsaro suna bukatar su dauki mataki cikin gaggawa cikin hanzari kan wannan kungiya domin hana yaduwar tashin hankali da rashin kwanciyar hankali a yankin Arewacin Najeriya tunda duk masifun da futintinun daganan suke fitowa.
Muna kira da gwamnatin data dubi kirman Allah ta dubi talakawanta da sanin cewa Allah ita zai tambaya akan haka domin ta kasa kare talakawa ta dubi wannan al’amari da ayi gaggawar magance su kafin su yadu.
Hajiya Rukayya
Assalamu Alaikum,
Ya aiki ya kokari Allah ya taimakeku amin, nidai gaskiya Ra,ayina agameda wannan sabuwar Kungiyar ‘yan ta,adda data fito ajahar kebbi maisuna Lakurawa shine gaskiya gazawar Gwamnatice, gwamnati kiji Tsoron Allah, kutuna sai da kukayi rantsuwa da Alkar’ani akan zasu kare hakkin jama’a da dukiyoyinsu, to ya kamata kuyi kokari ku daure ansan abin akwai wahala talaka suna karkashinku kuma kune gatanmu a duba wannan lamarin da adakatar dasu tun kafin suyi karfi su gagari mutane kunsan Hausawa suna cewa ice tun yana danye ake tankwarashi idan ya ruka bazai tankwaru ba saidai ya karye. Allah ya kawo mana mafita nagode.
Habiba Tijjani
Assalamu alaikum!
Nidai duk da dai bansan kunkiyarba, ra’ayina akan wannan kungiyar ‘yan ta’adda da tafito a Kebbi mai suna Lakurawa to a gaskiya ni bana goyon bayan wannan kungiyar domin duk abin da za’ace ta’addanci ne to abu ne wanda yake da muni ga rayuwarmu mu mutane tunda abu ne wanda za’azo ayi ta fadace fadace da kashe kashe a rayuwa, za’azo ana ta asarar rayuka ko kuma mutane su zama cikin wahala da tashin musamman ma talakawa domin su sukafi shan wahala a irin wannan hali idan ya taso a gaskiya ni bana goyon bayan wannan kunkiyar, muna rokon gwamnatin da ta taimaka ta tallafa cikin gaggawa tun kafi kungiyar ta yi karfi a samu a rushe wannan kungiyar idan wani abu suke nema a neme su a sasanta da a rushe wannan kungiyar idan wani abu suke bukata domin a kawo karshen wannan kungiya to a taimaka a musu. Allah ya sa mudace.
Fatima Abdullahi
Assalamu alaikum
Ni dai a gaskiya ra’ayina akan wannan sabuwar kungiyar mai suna Lakurawa a gaskiya duk wani mutum musulmi mai hankali wanda yake a nan kasarmu ta Nijeriya duba da yanayi da halin da muke ciki bamu kama da Boko Haram ba sannan ga garkuwa da mutane duk ba’a gama da su ba sannan a ce ga wata kuma ta fito ban da kuncin rayuwa da fama da mutane suke ciki sannan kuma a ce ga wata kunkiya ta sake fitowa gaskiya wannan al’amari abin dubawa ne. Babu wani mutum Musulmi a Nijeriya da zai goyi bayan wannan kungiyar.
Ni a ra’ayina gaskiya ba na goyon bayan wannan kungiyar domin duk abin da za’a ce zai jefa Musulmi cikin wahala da tashin hankali ai ba abin so bane, kuma daga karshe kome kan talaka zai kare. Don Allah muna kira ga gwamnatin da babbar murya da ta duba wannan lamari ta yi kokarin kawo mana karshen wadannan ‘yan ta’adda tun kafin abin ya yi karfi in sha Allahu babu abinda zai gagari gwamnati indai an sa hannu.
Mu kuma talakawa mu taya gwamnatin da jami’an tsaro da addu’a Allah ya kawo mana karshe wadannan kungiyar Allah ya nakasasu.