Game da ziyarar da kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na kasar Sin, wasu gwamnatocin kasashe sun fitar da sanarwoyi, inda suka jaddada matsayinsu na bin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Sun kuma nuna adawa da danyen aiki da Amurka ta yi, na keta dokokin kasa da kasa, da keta ikon mulkin kasar Sin, da mallakar cikakkun yankunanta.
A ranar jiya Alhamis, Shugaban Sri Lanka Ranil Wickremesinghe, ya nanata alkawarin nuna goyon baya ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da mutunta manufofin kare ikon mulkin kasashe, da mallakar cikakkun yankunansu, karkashin yarjejeniyar MDD.
A nasa bangare, mataimakin shugaban taron tsaro na Rasha Dmitry Anatolyevich Medvedev ya nuna cewa, ziyarar Nancy Pelosi a yankin Taiwan tsokana ce, wadda ta lalata tsaron Asiya kai tsaye. A hannu daya kuma, wai bangaren Amurka ya nuna tsaiwa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kaza lika hakan ya tunzura dakarun ’yan aware ta hanyoyi daban daban.
Shi ma mataimakin shugaban harkokin wajen kasar Sudun ta Kudu Hon. Deng Dau Deng Malek ya nuna cewa, Sudan ta Kudu tana tsaiwa tsayin daka, kan ka’idar rashin tsoma baki cikin harkokin gidan juna, tana kuma fatan ci gaba da tsaiwa tsayin daka ga goyon bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
Bugu da kari, kasashen Tanzania, da UAE, da Qatar, da Sao Tome da Principe, da Dominica, da sauran kasashe, su ma sun nanata tsayawa tsayin daka kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma mutunta ikon mulkin kasar Sin, da mallakar cikakkun yankunanta. (Safiyah Ma)