An fitar da tsarin aikin bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin raya masana’antu, da hada hadar rarraba hajoji na Beijing a hukumance, yayin bikin bude taron baje kolin hajojin dake shiga sassan kasuwannin duniya karo na biyu da aka kaddamar yau Talata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Tsarin ya tattaro dabarun cin gajiyar dukkanin damammaki na hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki na dijital, da cinikayya ta yanar gizo tsakanin kasashe, da gaggauta binciko hanyoyin morar fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama a masana’antu, da kafa managarcin tsarin tattalin arziki na dijital mai game da dukkanin sassa, da kara fadada karsashin daga darajar tsarin shigar da hajoji kasuwannin kasa da kasa.
- Tinkarar Sauyin Yanayi Na Bukatar Gaggauta Sauke Nauyin Da Ya Rataya A Wuyan Kasa Da Kasa
- Yahaya Bello Ya Fada Komar EFCC, Zai Amsa Tambayoyi
A lokaci guda kuma, tsarin zai ingiza ayyukan kirkire-kirkire na fasahohi marasa gurbata muhalli, da yayatawa, da cin gajiyar dabarun samar da ci gaban daukacin masana’antu bisa salon kyautata muhalli.
A bikin baje kolin hajojin na bana, mahalarta da dama sun jinjinawa kasar Sin, bisa muhimmiyar rawa da take takawa tare da sauran sassa, wajen wanzar da daidaito da kyautata tsarin shigar da hajoji kasuwannin kasa da kasa, da fuskantar matakan kara zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)