Kasar Sin na sa ran yawan masu amfani da fasahar sadarwa ta 5G zai wuce kashi 85 cikin dari nan da karshen shekarar 2027, yayin da kasar wacce ta kasance mafi girman tattalin arziki na biyu a duniya ta gaggauta yin amfani da fasahar ta 5G a sassa da dama.
Hakan na nufin za a samu tashoshi 38 na 5G ga ko wadanne mutane 10,000, yawan bayanan da ake musaya ta kafar intanet din hannu bisa fasahar ta 5G zai kasance kashi 75 cikin dari, kuma adadin tashoshin manyan kwamfutoci da aka hada da fasahar 5G a kasar zai wuce miliyan 100, kamar yadda tsarin aiki da ma’aikatun gwamnatin Sin suka tsara ya bayyana.
- Tinkarar Sauyin Yanayi Na Bukatar Gaggauta Sauke Nauyin Da Ya Rataya A Wuyan Kasa Da Kasa
- Rundunar ‘Yansandan Katsina Ta Daƙile Yunƙurin Sace Mutane, Ta Ceto Mutane 14
Hakazalika, yawan amfani da fasahar 5G a masana’antu manya da matsakaita zai kai kashi 45 cikin dari a karshen shekarar 2027, bisa ga tsarin aikin da aka fitar a ranar Litinin.
Za a yi matukar sa kaimi ga habaka na’urori masu aiki da fasahar 5G a babban mataki, da gaggauta bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da saukake yadawa da aiwatar da sabbin fasahohin zamani, da karfafa sabbin karfin ingiza tattalin arziki da ci gaban zamantakewa mai inganci. (Yahaya)