Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya gurfanar a gaban Babbar Kotun Abuja a ranar Laraba kan zargin almundahanar kudade.
Hayaniya ta barke a cikin kotun bayan magoya bayan Bello sun cika kotun makil, wanda ya sa Mai Shari’a Maryann Anenih ta bar kotun a fusace.
- Ana Kashe Sama Da Dala Biliyan 1 A Shekara Wajen Yaki Da Cutar Zazzabin Cizon Sauro – Minista
- ‘Yansanda Sun Ceto Fasinjoji 14 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
Ta ce ba za ta dawo ba har sai an samu tsari da nutsuwa a kotun.
Bello, ya hanzarta shiga lamarin, inda ya roki magoya bayansa su fice daga kotun.
Wannan matakin ya kwantar da hatsaniyar da aka samu, inda mutane suka fice daga kotun.
Don tabbatar da oda, Bello ya tsaya a bakin kofar shiga kotun yana sanya ido don tabbatar da cewa magoya bayansa sun bi umarnin kotun.
Ana tuhumar Bello kan tuhume-tuhume 16 da suka hada da karkatar da kudade da almundahana.